Mutahhari Da GwagwarmayaDukkan Kungiyoyi na da Hannu a Juyin
Allama Shahid Muratadha Mutahhari ya bayyana cewa juyin Musulunci a Iran bai takaita da wani gungu na mutane su kadai a Iran ba, bai kuma kadaita da ma'aikta (kamar juyin Faransa) ko manoma (kamar juyin da ya faru a Rasha a wani lokaci da ya wuce) ba; haka juyin ba na 'yan jami'a ko 'yan kwadago kawai ba ne. Maimakon haka, in ji Allama, shi juyi ne da talaka da mawadaci, mace da namiji, dan birni da dan kauye, dalibin jami'a da malamin addini, mai ilimi da jahili duk suka hadu suka gudanar da shi daidai wa daida. Ya ce tasirin bayanan shugbannin juyin daidai ne a wajen mutane.[13] Manufofin Juyin Musulunci Na Iran
Wani abu mai mahimmanci da zai iya nunawa mai sauraro irin yadda Ustaz al-Shahid ke la'akari da gwagwarmayar kawo sauyi, shi ne yadda ya kalli manufofin juyin Islam. A yayin bayyana manufofin juyin Islam, ya bijiro da wasu tambayoyi ne kamar haka: shin wace manufa juyin Islam a Iran ke nufi? Shin Dumukuradiiya ake nufi? Shin so ake a yanke hannun 'yan mulkin mallaka daga Iran? Ko so ake a kare abin da ake kira yau da hakkin dan Adam? Shin ana son gamawa da rashin adalci da magance fifita wani sashi a kan wani bisa zalunci ne? Shin ana son tsige tushen zalunci ne? ko so ake a yaki bautar duniya? Ko me ake nufi? Amsar wadannan tambayoyi suna tabbata idan aka yi la'akari da asasan wannan juyi da bayanan da shugabannin juyin suka yi ta yadawa; amma a dunkule, in ji Allama, ana iya amsawa da "I" da "a'a". 'I' cewa duk wadancan wani sashi ne daga manufofin juyin. Kuma a'a, manufofin juyin musulunci basa iyakantuwa da wadancan bukatu; domin juyin Musulunci manufofinsa ba iyakantattu ba ne; domin Musulunci baki dayansa gamamme ne da ba a daidaita shi; kuma Musulunci ba ya karewa da isa zuwa wadancan manufofi. Amma wannan ba ya nufin cewa ta fuskar tsare-tsare da dabaru juyin Islama ba ya gabatar da wasu manufofi, ko ba ya lura da matakan cimma manufofin. Ustaz al-Shahid ya ci gaba da fitar da manufar gwagwarmayar Musulunci daga Nahjul-Balagha, inda ya fitar da zancen Imam Ali (alaihis-salam) mai cewa: Don mu dawo da dokokin addininKa, kuma mu bayyana gyara a garuruwanKa; ta yadda wanda ake zalunta daga bayinKa zai aminta; kuma a tsayar da haddodinKa da aka daina aiki da su.[14] A karshe Shahid Murtadha Mutahhari ya bayyana cewa duk mai aikin kawo gyaran da iya samun nasarar aiwatar da wasu ka'idoji hudu, to kuwa zai yi nasara. Wadannan ka'idoji kuwa su ne: 1-Ya iya fuskantar da tunane-tunane da ra'ayoyi zuwa Musulunci na asali, kuma ya iya karya bidi'o'I da karakace-karkace daga zukata. 2-Ya iya samar da kyakkyawan sauyi a rayuwar gama-garin mutane, ta hanyar samar musu da abinci, matsuguni, kiwon lafiya, ilimi da tarbiyya. 3-Ya iya tabbatar da cewa ka'idojin daidaitawa da 'yan'uwataka shi ke shugabanci cikin alakokin zamantakewa tsakanin mutane. 4-Ya tabbatar da dokokin Allah da shari'ar Musulunci a cikin al'umma.[15]
|