Mutahhari Da Gwagwarmaya4-Imani da Musulunci da dogara da shi. 5-Yaki da mulkin-mallaka daga waje. 6-Kira zuwa ga hadin kan Musulmi. 7-Samar da ruhin jihadi a cikin al'ummar Musulmi. 8-Magance matsalar jin rauni a gaban Turawa da ya addabi Larabawa. Har ila yau Shahid Mutahhari ya bayyana manyan manufofin Sayyid Jamauddin al-Afgani kamar haka: 1-Musulmi su zama wayayyun mutane, wadanda suka san zamunansu, suka kuma lakanci sana'o'in zamani. 2-Samar da wata al'ummar Musulmi 'yantacciya, wadda ta kubuta daga duk wani kang na harshe, yanki, mazhaba ko wani abu daban; wadda mutanenta suke 'yan'uwan juna. 3-Kubutar da Musulmi daga tabaibayin 'yan mulkin mallakan wajen da 'yan kama-karyan cikin gida. 4-Musuluncin asali na Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa'lihi), wanda ya tsira daga duk wasu jone-jone da shige-shigen ra'ayoyin mutane, ya zama shi ke hukunci cikin mutane.
|