Mutahhari Da GwagwarmayaMatsalolin al'umma da suka yunkurar da Sayyid Jamaluddin, kamar yadda Ustaz al-Shahid ya hakaito, sun ne: 1-Mulkin kama-karya dake gudana a cikin garuruwan Musulmi. 2-Jahilci da rashin wayewa dake addabar Musulmi, da matsanancin ci-baya a ilmance da yanayin zamantakewa da suke fama da su. 3-Yaduwar miyagun akidu cikin tunane-tunanen Musulmi, da nisantarsu da Musuluncin asali na hakika. 4-Rarraba tsakanin Musulmi ta fuskar mazhabobi da wasu al'amura da ba su shafi addini ba. 5-Mulkin-mallaka da ya yi musu kabe-kabe a gaba. Sayyid Jamaluddin ya yi bakin kokarinsa wajen fitar da hanyoyin magance wadancan matsaloli. Ya yi amfani da abubuwan da suka samu a lokacinsa, irin su tafiye-tafiye, alakoki, laccoci, yada littafai da buga mujallu da kirkirar kungiyoyi da mu'assasosi dabam daban don aiwatar da ayyuka a wannan fanni. A takaice hanyoyin da Ustaz al-Shahid ya bayyana cewa Sayyid Jamaluddin ya bi wajen magance matsalolin duniyar Musulmi a lokacin sun ne: 1-Yaki da son-kan 'yan kama-karya. 2-Ganimantuwa da ilumma da sannai na zamani. 3-Komawa ga Musulunci na asali.
|