Mutahhari Da Gwagwarmaya



Ya bayyana cewa babu wasu gwaraza fitattu daga kasashen larabawa in ba wadannan ukun ba. In ma wasu sun bayyana, to wadanda suka ci gaba da hanyar da shi Sayyid Jamaluddin al-Afgani da Muhammad Abduhu da Sheikh AbdulRahman Kawakibi suka fara ne, kuma ambatonsu bai karfafa ba. Ya ci gaba da bayanin cewa akwai wasu mutane a kasashen larabawa da suka yi da'awar kawo gyara da gwagwarmaya irin su AbdulHamid bin Yadis daga Algeira, da Tahir al-Zahrawi daga Syria daAbdulKadir daga Maroko da Jamaluddin al-Kazimi daga Syria da wasun wadannan, illa ba su iya aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata ba. A nan Shahid al-Allama tambayoyi ya yi game da abin da ya haifar da haka da cewa: mai ya sa wasu mutanen banda wadancan ukun, wadanda za mu iya dauka a matsayin gwarazan kawo sauyi, ba su bayyana ba a kasashen larabawa? Kuma wadanda suka bayyana mai yasa ba su yi aikin ta ingantacciyar hanya ba? Tun farko ma, mai yasa ruhin gwagwarmaya ya yi rauni a garuruwan Musulmi, masamman larabawa? Mai ya sa kungiyoyin kabilanci na larabci da irin su jam'iyyar Ba'ath da tunanin gurguzu suka fi tasiri a zukatan matasan larabawa fiye da gwagwarmaya?

Amsar da ya ba wadannan tambayoyi ne ke da mahummanci gare mu, kuma suke kara bayyana mana irin yadda yake kallon mabubbugar tunanin gwagwarmaya.Ya ce:

Yayin amsa wadancan tambayoyi kowa na iya kawo amsarsa bisa dogaro da dalilansa na masamman. Amma ni, a kashin kaina, ina ganin babban dalilin da ya sanya gwagwarmayar Musuluncin da Sayyid Jamaluddin al-Afgani ya fare shi ya rasa mahimmancinsa da tunzurarwarsa shi ne yadda mafi yawan masu da'awar kawo gyara, bayan Sayyin Jamaluddin da Muhammad Abduhu, suka rungumi akidar Wahabiyanci, da yadda suka kange kawunansu a kuntataccen tsaiko nan na tunanin wannan tafarki (na Wahabiyanci). Wadannan sun sauya waccan gwagarmaya ta kawo gyara ne suka mayar da ita gwagwarmayar Salafiyya; sannan yayin binsu ga Sunna din ma suka sauko zuwa bin Ibin Taimiyya. A hakika sun sauya ka'idar nan ta komawa zuwa ga Musulunci na hakika zuwa komawa zuwa ga Hambaliyya, wadda ake dauka daga cikin mazhabobi marasa zurfin mahanga a Musulunci. Da haka sai suka juya akalarsu daga fito-na-fito da 'yan mulkin mallaka da 'yan kama-karya zuwa yaki da akidun da suka saba da na Hambaliyya masamman na Ibin Taimiyya.[11]

MALAMAN SHI'A DA AKIDAR GWAGWARMAYA

Ya zuwa yanzu duk abin da muke magana kan tunanin kawo sauyi da gwarazan gwagwarmaya a duniyar Musulmin Ahlusunna. Sai dai ana da sabani a kan ainihin mazhabar Sayyid Jamaluddin al-Afagani, wasu sun tafi a kan cewa shi Ahlusunna ne, wasu kuwa suka ce shi Shi'a ne. Ko ta halin kaka dai, Allama Shahid Mutahhari na daga cikin wadanda suke ganin shi Shi'a ne.; don haka, kamar yadda ya fada da kan shi, ya kawo shi cikin jerin mujaddadan Sunna ne saboda mafi yawan aikace-aikacen shi a garuruwansu ya aiwatar da su.

Amma dangane da yunkure-yunkuren kawo gyara a tsakanin 'yan Shi'a, wannan ya saba kwata-kwata da yadda yake a tsakanin 'yan Sunna a ra'ayin Allama Shahid Murtadha Mutthhari; domin a wajen Shi'a wannan aiki na daukar wani salo ne na daban. Sai dai duk da haka, su ma sun ja-goranci yunkure-yunkuren kawo gyara dake bisa tsari, kuma wanda ya haifar da natija. Shahid na ganin tsarin 'yan Shi'a na kawo gyara ya fi zurfi kwarai da tushe. Har ma yake cewa:

Ba ma ganin yunkure-yunkuren kawo gyara irin yunkurin Tabacco a tsakanin Ahlusunna, wanda aka kalubalanci mulkin mallakar Biritaniya karkashi ja-gorancin malaman addini; wanda kuma shi ne ya haifar da karewar wani mulki na kama-karya a Iran.[12]

Haka, In ji Shahid, ba ka ganin sauyi irin sauyin nan na thauratul-Ishrin na Iraki, wanda ya kalubanci wani shiri na 'yan mulkin-mallakan Birtaniya a kan wannan kasa ta Musulmi; wanda shi ne ya haifar da samun 'yancin Iraki. Ko irin sauyin nan na thauratul-dostur mai kalubalantar kama-karyan mahukuntan Iraniyawa; ko irin yunkurin da ya haifar da gwamnatin Musulunci ta yanzu a Iran, wanda malamai, karkashin ja-gorancin Imam Khumaini, suka ja-goranta.

Duk wadannan yunkure-yunkure sun faru ne a hannun malaman Shi'a, wadanda a lokuta da dama, kamar yadda Ustaz al-Shahid ya tabbatar, da wuya za ka ji suna zantuka kan gwagwarmaya. Misali yunkurin Tabacco da malaman Shi'a suka fare shi a Iran, nasararsa ta kasance ne a hanun babban marja'in Taklidi al-Haj Mirza Hassan al-Shirazi. Thauratul-Ishrin kuwa da malaman Shi'a a Iraki suka fare shi don yakar turawan mulkin-mallakar Ingila, ya kasance ne karkashin ja-gorancin babban mujtahidi Sayyid Mir Muhammad Taki al-Shirazi. Thauratul-dostur kuwa da ya faru a shekarar miladiyya ta 1905, ya kasance ne karkashin ja-gorancin Mulla Muhammad Kazim al-Khurasani da Sheikh Abdullahi al-Mazandarani, wanda ke cikin malaman Najaf a wannan lokacin. Har ila yau wasu manyan malamai biyu na da matukar tasiri a wannan yunkuri na dostur, in ji Allama al-Shahid, wadannan kuwa su ne Sayyid Abdulllahi al-Bahabahani da Sayyid Muhammad Tabataba'i.

JUYIN MUSULUNCI A IRAN

Ya zuwa yanzu za mu iya kusantar inda muka dosa a wannan kasida. Domin mun matso kusa kwarai, inda zamu duba yadda Ustaz al-Shahid ke kallon juyin Musulunci da ya fara tun a shekara ta 1963 a Iran, kuma ya sami nasara a watan Febrarun shekarar miladiyya ta 1979.

Ya zama dole a nan mu fadi cewa: abin da kowa ya sani ne cewa, juyin Islama da ya sami nasara a kasar Iran, wanda a sakamakonsa aka kifar da daya daga cikin miyagun gwamantocin 'yan kama-karya da karnukan farautar Yamma, ya tabbatar da hasahen masu gwagwarmaya na yakinin samun nasara a karshe. Juyin ya canza akalar duniyar Musulmi, kuma ya zama ja-gora wajen haskaka zukatan 'yantattu a ko'ina cikin duniyar Musulmi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next