Mutahhari Da Gwagwarmaya



Manyan bambance-bambancen dake tsakanin Shiekh Muhammad Abduhu da Sayyid Jamaluddin abu biyu ne:

1-Sayyid Jamaluddin na ganin wajibcin bore da juyin-juya hali; alhali Sheikh Muhammad Abduhu na ganin kamata ya yi a bi a hankali.

2-Sayyid Jamaluddin na ganin kamata ya yi a matakin farko a fara da kalubalantar 'yan mulkin mallaka da 'yan kama-karya; domin dole ne a tsige tushen fasadi daga tushensa tun farko; alhali Sheikh Muhammad Abduhu, masamman a karshe rayuwarsa bayan ya koma Masar, yana ganin tarbiyya da karantarwa shi ne aikin farko kafin dulmiya cikin tsagwaron harkokin siyasa. Wannan bambanci, ta iya yiwuwa ya samo asali ne a kan kasancewar abin da kowane daya daga cikin wadannan manyan mutane biyu ya yi ya cika na dayan ne; wannan kuwa bayan ganin duk sun hadu a kan:

1-Wajibcin komawa zuwa ga mabubbugar asali ta Musulunci da kalubalantar tushen karkacewa.

2-Fassara hukunce-hukuncen Shari'a da abin da ya dace da zamani, sabanin rufe ido da bin duk hanyar da magabata suka bi ba tare da tantancewa ba.

3-Nisantar rarraba da kungiyanci.

4-Ta'akidi a kan raya asalin ijtihadi da bude kofarsa.

5-Kokari wajen sanin ruhin addini na hakika; sabanin busasshen kallon da aka saba da shi a da.

Bayan wadannan bayin Allah biyu akwai manyan 'yan gwagwarmaya biyu daga Ahlusunna da Allama Murtadha Mutahhari ya yi nazari a kansu; wadannan kuwa su ne Sheikh AbdulRahman Kawakibi, dan kasar Syria. Da Ikbal Lahori dan kasar Indiya. Inda za mu dauki kowane daya mu dubi yadda Ustaz al-Shahid ya kalle shi da mun kara samun haske a kan nazarce-nazarcen shi a kan yunkurin Musulunci a karnonin baya-baya nan. Sai dai haka ba zai yiwu ba; na farko saboda karancin lokaci, na biyu kuma saboda haka zai sa mu fita daga haddin abin da muke magana a kai.

Sai dai ya zama dole a nan mu dan yi ishara da wani al'amari mai mahimmanci da Shahid al-Allama ya fada dangane da guguwar sauyi da ta taso a kasashen Musulmi daga baya-bayan nan.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next