Mutahhari Da Gwagwarmaya



YUNKURE-YUNKUREN KAWO GYARA A TARIHI

Banda tarihin Manzo (sallallahu alaihi wa'alihi) da Imaman Ahlulbaiti sha biyu (alaihimus-salam), wannan tarihi dake cike da darussa da shiryarwa, za mu sami tarihin Musulunci cike da yukure yunkuren kawo gyara fiye da kowace al'umma, in ban da cewa kawai tarihin na mu ne bai ba wannan janibin hakkin da ya kamace shi na bincike da nazari ba.

Tun akalla shekaru dubu da suka wuce tunanin bayyanar Muajaddadi da Mai Raya addini, a farkon kowane karni,ya fara yaduwa a tsakanin Ahlusunna da farko, sannan 'yan Shi'a. Ahlusunna na riwaito wani hadisi daga Abu Huraira dake cewa:

A farkon kowane karni Allah zai tayar wa wannan al'umma da wanda zai jaddada mata addininta.[5]

Duk da cewa ba a la'akari da isnadin wannan hadisi, ta fuskar tarihi kuma ba a karfafa shi ba, sai dai yaduwar irin wannan tunanin da karbuwarsa a tsakanin Musulmi yana bayyana yadda Musulmi ke jiran mai kawo gyara ko masu kawo gyara a farkon kowane karni; ta yadda wannan ya sa ma'abuta kowane yunkuri da bore a tsakaninsu na sa kansu a wannan matsayi.

A takaice dai muna iya cewa: A ra'ayin Shahid Allama Mutahhari, "Islahi, mai Islahi, yunkurin kawo gyara da jadadda addini, kamar yadda ake kiransa daga baya-bayan nan, duk wasu sanannun abubuwa ne a tsakanin Musulmi.[6] Wannan ya sa Shahid ke ganin cewa nazari na bin diddigi dangane da yunkure-yunkuren kawo gyara ko harkat al-Islamiyya a tarihance abu ne mai matukar afani, bisa fatan da ya yi na cewa wadanda ke fagen wannan aiki na Annabawa zasu tabbatarwa kansu da na natijar da ake bukata.

Abu ne na daabi'a cewa yunkure-yunkuren da suka nemi kawo gyara ba su kasance daya ba, kuma ba dukansu ne suka kawo gyaran ba. Wasu daga cikin su sun yi da'awar kawo gyara, sun kuma yi aiki a kan haka bias hakika. Amma wasu sun yi amfani ne da sunan kawo gyara wajen kawo fasadi. Yayin da wasu suka fara daidai, amma sai suka karkace daga kasashe.[7]

Yunkure-Yunkuren Alawiyawa

Shahid al-Allama ya bayar da misali na farko a wannan babi na yunkure-yunkuren kawo gyara a tarihi da yunkure-yunkuren Alawiya a lokutan Khalifancin Umayyawa da Abbasiyawa, inda ya ga cewa mafi yawan wadannan yunkure-yunkure sun kasance: "na kawo gyara ne", sabanin wasu yunkure-yunkure masu yawa wadanda muninsu ya kai ga sun kalubalanci Musuluncin ne ma baki daya! Dalilin da ya sa Allama ya kira wadancan yunkure-yunkure na Alawiyawa da cewa mafi yawansu na kawo gyara ne, shi ne saboda la'akari da yadda suka iya girgiza fushin al'umma a kan mahukuntan Abbasiyawa ja'irai.

Yunkurin Shu'ubiyya

Wannan wani yunkuri ne da ya kasance na kawo gyara da farkon al'amarinsa, yayin da ya riki taken Ya ku mutane, hakika mun halicce ku ne daga Namiji da Mace, sai muka sanya ku al'ummu da kabilu (dabam daban) don ku san juna. Lallai mafificin ku a wajen Allah shi ne wanda ya fi ku takawa wajen kalubalantar bambance-bambancen Umayyawa. Akidarsu ta daidaitawa ne ma yasa aka rika kiransu da Ahalul-Taswiyah. Saboda kuma sun riki waccan aya ta AlKur'ani ya sa ake kiransu Shu'ubiyyah. Sai dai wani abin takaici shi ne suma mabiya wannan tafarki sun fada cikin tarkon abin da suke yaka, yayin da suka karkace suka zama kungiyar kabilanci; wannan ya sa muminai daga cikin su masu son gaskiya da bin Musulunci daidai suka janye. A karshe ma dai mahukuntan Abbasiyawa ne suka rika amfani da wannan kungiya wajen cinma manufofinsu.

Yunkurin Kawo Gyara Aiki Ne Na Zamantakewa Ko Na Tunani?

Allama Mutahhari ya bayyana cewa wasu daga cikin yunkure-yukuren kawo gyara na Musulunci sun kasance na tunani ne, yayin da wasu suka kasance na zamantakewa. Wato na farkon na kawo sauyi ne na tunani, yayin da na biyun ke kawo sauyi cikin mutane; wasu kuma duka biyun suka hada. Ya bayar da misali da yunkurin Ma'adumin wajen kalubalantar Mangul a Sibzawar dake Khurasan a matsayin yunkurin sauya al'umma. Haka ya bayar da misali da yunkurin Ikhwanul-Safa a matsayin yunkurin sauya tunani.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next