Mutahhari Da Gwagwarmaya



Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Wannan kasida, cikin yardar Allah, zata yi kokarin nazari ne a kan Yunkurin Musulunci har zuwa karni na ashirin da daya.

Yunkurin Musulunci shi ne abin da 'yan'uwa a nan bangaren ke kira da Gwagwarmayar Musulunci; wanda a turance aka san shi da Islaminc Movement; a labarbce kuma al-harkatul-Islamiyyah.

Al'amarin 'Gwagwarmaya' babba ne mai fadin mahanga. Ba al'amari ne da ya ta'allaka da wasu mutane banda wasu ba ko wata kasa banda wata. Gamammen al'amari ne da ya shafi rayuwar kowane Musulmi, ya sani ko bai sani ba.

Don haka kasidar ta dauki wani dan karamin bangare ne daga wannan al'amari mai mahimmancin gaske. Za ta waiwayi yadda babban malami, manzarci, masanin addini da rayuwa, Ayatollah, Allama, Ustaz, Shahid Murtadha Mutahhari ya kalli gwagwarmayar Musulunci: ta'rifinta, iyakokinta, tarihinta da abubuwan da suka kamata mai bin wannan tafarki ya lizimta; duka a takaice. Allah muke roko da ya sa mu dace, Ya kuma kyautata niyyoyinmu.

Ta'arifi

Ustaz al-Shahid, Muratadha Mutahhari (RA) ya kalli yunkurin gwagwarmayar Musulunci a matsayin reshe ne na aikin kawo gyara al-Harka al-Islahiyyah; wanda ba dukkan shi ne gwagwarmayar Musulunci ba.

Kalmar Islahi kalma ce ta larabci, dake nufin 'tsari', 'daidaitawa' da 'gyarawa'. Kishiyar kalmar ita ce Ifsadi, wato 'lalatawa', 'watsawa' da 'batawa'.[1] Wannan zai sa a iya ta'arifin Islahi, a shar'ance da: "aikin da yake nufin tsara al'murran mutane, a daidaikunsu ko a jama'arsu, a matsayin su na iyali, anguwa, gari, kasa ko al'umma."

Akur'ani mai girma ya yi amfani da wannan kalma a kan duk wadannan ma'anoni[2], har da ma'anar: "gyara al'umma", wanda shi ne mahallin maganarmu. AlKur'ani ya kira Annabawa da Muslihun, wato masu kawo gyara.

Kira zuwa ga kawo gyara kuwa ruhi ne na Muslunci, in ji Ustaz al-Shahid. Kum kowane Musulmi, a matsayin shi na Musulmi, mai kira ne zuwa ga islahi a farkon farawa, ko: "akalla yana daga masu goyon bayan kira zuwa ga Islahi.[3]" Wannan kuwa saboda kira zuwa ga Islahi, banda kasancewarsa sifar Annabawa da Manzanni, daya ne kuma daga cikin daidaikun horo da aikin kirki ne da hani da mummuna (al-Amru bil-ma'arufi Wal-Nahyu anil-munkari), wanda ke cikin rukunin zamantakewa cikin karantarwar Musulunci[4].

Kawo Gyara Ko Hidima Ga Jama'a

A wannan zamanin, in ji Allama, mun ga yadda kawo gyara cikin al'umma ya sami wani babban matsayi a wajen mutane, har suka shiga ba shi muhimmanci; wannan wani abin yabo ne. Sai dai wasu kan wuce iyaka; yayin da suke ganin cewa duk wani aiki ko hidima in dai bai shiga cikin abin da suka kira da aikin kawo gyara cikin al'umma ba, ba shi da wata kima; suke ganin cewa matsayin kowane mutum ya ta'allaka ne da irin yadda ya lizimci aikin kawo gyara cikin al'umma. Irin wannan tunani, a ganin Ustaz al-Shahid, ba ingantacce ba ne. Domin gano maganin sankara (cancer) hidima ce duk da kuwa ba aikin kawo gyara ga al'umma ba ne. Samar da ci-gaba na ilimi hidima ce alhali ba aikin kawo gyara cikin al'umma ba ne. Likitan dake aiki dare da rana don warkar da marasa lafiya, yana aiwatar da hidima ne ga al'umma; amma ba aikin gyara al'umma yake yi ba. Dalilin haka kuwa, kamar yadda Shaikh al-Shahid ke gani, shi ne saboda aikin gyara al'umma na nufin: "Sauya zamantakewar mutane zuwa manufar da ake bukata"; ayyukan wadancan kuwa ba haka suke ba; don haka bai kamata mu ki yabon ayyukan wadancan ba bisa da'awar cewa ba su taka wata rawa wajen ayyukan kawo gyara cikin al'umma ba. Alal missal, ayyukan Sheikh Murtadha al-Ansari, wanda daya ne daga cikin manyan fakihai; ko na Mulla Sadra, wanda daya ne daga cikin manyan masana falsafa Musulmi, duk manyan hidimomi ne masu matukar daraja, a daidai lokacin ba ayyukan kawo gyara ba ne.

Shahid al-Allama ya yi bayani da cewa ayyukan Annabawa, Manzanni da Imamai shi ne kawo gyara, a fagage dabam daban na siyasa, tattalin arziki da zamantakewar mutane baki daya. Don hak a wurare dabam daban aka kira su da Muslihun. Imam Ali (alaihis-salam) mai kawo gyara ne. Haka Imam Hasan (alaihis-salam) cikin sulhusa da Mu'awuya, haka Imam Husaini yayin arangamarsa da Yazid, haka….haka….



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next