Kurkuku Bincike Da Hukunci



Wannan halarcin ya zo a Littafin Alkur’ani mai girma da kuma Hadisai madaukaka na Annabi mai tsira da aminci, da kuma Ijma’in malamai a dunkule, amma a hankali hankali yana hukuncin wajabcin kare tsari da kare hakkoki da kiyaye su da kula da maslaha ta gaba dayan al’umma, wannan kuwa ba shi yuwuwa sai da hukuma mai adalci mai tsaida dokoki da hana barna wanda furzin yana daya daga cikinsu ne, tsare mai laifi duk da a hankali ya saba da ‘yancin dan Adam na yana da iko a kan kansa da ransa da walwalarsa amma hankali yana hukunci da wajabcin gabatar da fara kare da kiyaye maslaha ta gaba dayan al’umma a kan maslahar mutum daya wato shi mai laifi.

 

FARKON WANDA YA GINA FURZIN

Kamar yadda ya gabata furzin a lokacin Manzo (S.A.W) yana nufin tsarewa koda a masallaci ne ko soro ko a gidan mai laifi, shi ya sa aka yi bincike a kan cewa waye ya fara gina Gidan Sarka.

Abin da ya tabbata shi ne Umar Dan Khaddabi shi ne farkon wanda ya fara kirkiro furzin a tarihin Musulunci, koda yake Siyudi a littafin Ahkamus sujun ya danganta wannan zuwa ga Imam Ali (A.S). Kuma mai littafin Ithafur Ruwat Asshalbi Alhanafi ya danganta wannan zuwa ga Imam Ali (A.S) yana mai cewa: Farkon wanda ya gina furzin shi ne Imam Ali (A.S), halifofi kafinsa sun kasance suna tsare mutane a Abar ne.

A wannan magana ta Asshalbi akwai karo da juna a fili yayin da yake cewa: Halifofi sun kasance suna tsare mutane a Abar[5] ne, wato yana nuni zuwa ga Halifa Umar da Usman, al’amarin da yake nuna an fara furzin a lokacin Umar ne.

Shi ya sa Asshaihul Manawi ya amsa tambayar da Suldan Abul Amlak Almaula Isma’il Ibn Shari Al-Alawi ya yi masu shi da Alkali Bardala da Ibn Rihal da cewa: Ta yiwu abin da Suyudi yake nufi da farkon wanda ya gina furzin shi ne Imam Ali (A.S), yana nufin yayin da ya ga Abar (ta saba da Musulunci saboda matsin da ke tare da ita, da cunkoson mutane da mummunan halin da ya gani, shi ya sa bai yadda da haka ba) sai ya gina gida na musmman domin sanya ‘yan furzin. Musamman da yake Abar ya fi kama da gidajen furzin da sauran manyan Dauloli da babu ruwansu da kula da hakkin dan Adam suke yi[6].

 

SAKAMAKON SABA WA SHARI’AR MANZO (S.A.W)

Daga cikin abin da sabawa nau’in furzin da shari’a ta yarda da shi abubuwa ne masu yawa da zamu kawo wasu saga cikinsu nan gaba kadan, mafi yawan mutune sun dauka sabawar abu ne mai sauki, kamar yadda wasu suke ganin muhimmi shi ne tsarewa kuma an tsare mai laifin, suna ganin ba dole ba ne ya zama kamar yadda Allah ya umarta![7] Wadannan mutane sun kasa fahimtar cewa dukkan hukuncin da Allah ya hukunta ba kawai don a bauta masa ba ne kawai, a’a, akwai maslaha da Allah ya sanya cikin hukunce hukuncen wanda su mutane suka jahilce su, inda babu wadannan maslahohin da ya halarta ke nan Ubangiji ya bautar da mu da aikata haram sai ya iya halatta mana haram[8].

Sabawa Allah da duniya dan Adam ta yi da shelanta tawayenta gareshi ta hanyar kin biyayya ga dokokin da ya aiko manzonsa da su ba tare da canji ba, da kuma kin biyayya ga wasiyyansa (A.S) ya sanya ba kawai kafirai ba har duniyar musulmi ta fada cikin bala’in da ba zai kare ba har sai ranar da suka dawo ma abin da Manzo (S.A.W) ya yi musu wasiyya da shi, don haka ne ma duk bala’o’i da suke faruwa a duniya wasu abubuwa ne da ba mamakin faruwarsu, misalin haka, kaucewa Gidan Sarka kamar yadda Manzo (S.A.W) ya zo da shi daidai yake da misalin sauran dokoki da ya zo da su aka ki biyayya gareshi a cikinsu, kamar auren mutu’a, da kashe mutane da yawa don kashe daya, da makamantan irin wadannan hukunce hukuncen masu yawan gaske.

Haka nan kada mu manta da cewa furzin a Musulunci an yi shi ne ba domin huce haushi ba kan al’umma sai domin gyara da tarbiyyatarwa, don haka ne idan ka ga furzin ya cika, laifuffuka suna daduwa na shiga furzin, ka tabbata imma dai ba a yi shi don manufar da Musulunci ya yi shi ba, ko kuma sam ba bisa sahihin tsari yake ba, kamar a yi shi domin sanya wadanda suke da sabani da shugaban kasa, wannan ba abin da zai kai sai ga daduwar masu sabani kamar yadda tajriba ta nuna a tarihin Akidu da Dauloli.

Irin abubuwan da suka faru sakamakon kaucewa nau’in furzin na shari’a sun hada da:

1. Tafiyar da karfin masu lafiya a banza:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next