Kurkuku Bincike Da Hukunci22. Wanda ya yi kisa da gangan idan ba a yi masa kisasi ba. 23. Ribatattun yaki. 24. Wanda ya azabtar da bawansa har ya mutu. 25. Wanda ya ‘yanta rabin bawansa da yake mallaka sai a tsare shi sai ya sayi daya rabin daga abokin tarayyarsa ya ‘yanta shi gaba daya[15]. 26. Kawali. 27. Wanda ya yi ridda daga Musulunci bayan an haife shi musulmi, wato lokacin da aka samu cikinsa ko aka haife shi dayan iyayensa ko dayan kakanninsa musulmi ne. 28. Barawon da aka yanke hannunsa ana tsare shi domin a yi masa magani. A kwai wasu mutane da a kan tsare su har mutuwa ko su tuba wadannan mutane su ne kamar haka: 1. Wanda ya yi sata ta uku (har sai salihancinsa da gyara ya bayyana). 2. Macen da ta yi ridda har sai ta tuba.
|