Kurkuku Bincike Da Hukunci



Musamman da yake mafi yawan laifuffuka da ake tsare mutane a kansu a shari’ar yau a Musulunci ba su cancanci tsarewa ba, sai a ajiye mutane masu lafiya majiya karfi ba aiki sai ya zama sun dade a furzin har su zama idan sun fito ba zasu iya wani aiki ba, wani yakan yi burin ya koma ya zauna ana ciyar da shi saboda an riga an lalata shi da tarbiyyar zaman banza ba aiki, kuma yanzu ba zai iya wani aiki ba.

2. Lalata ‘Yan Gidan Sarka:

Da yawa furzin kan hada mutane masu manyan laifi da masu kanana da marasa laifi da masu laifi da marasa laifi da an tsare shi bisa tuhuma, kamar wanda aka kama don kawai an gan shi da makami wanda tayiwu ya rike shi ne domin kare kansa, ko wanda wasu suka kulla musu sharri. Kamar yadda a kan hada yara da manya ko maza da mata da sauransu, a irin wadannan ayyuka akwai misalai da yawa da babu mahallin kawo su a wannan takaitaccen littafi. A nan ne zaka sami mutane da dama sun zama mujrimai masu laifi manya a duniya saboda ilimin da suka samu a wajan wasunsu a irin wannan mugun wuri.

3. Rashin amfanin matakan da a kan dauka:

Saudayawa matakan da a kan dauka domin hana laifuffuka zaka ga basu da wani amfani domin ba su hana sake maimaita laifin ga wanda aka daure, abin da yakan nuna gajiyawar irin wadannan matakai, sai ya zamana adadin ‘yan furzin da ya hada da masu komawa, da farin shiga, a kullum sai ninninkawa yake yi a duniya.

4. Kashe ruhin ‘yan Gidan Sarka:

Wannan kusan shi ne abin da muka yi nuni da shi a lamaba ta daya game da kashe ruhin son neman abin kai da aiki domin yawaita zaman banza a furzin da rashin aikin yi da ‘yar furzin ke fama da shi. Har ma kakan sami wani yakan ce : A ajiye masa wajansa domin ya je ya yi wani laifin ya dawo ya ci gaba da zamansa a furzin.

5. Dada kwarjini ga dan furzin:

Saudayawa wadanda suka fito sukan samu wani kwarjini a cikin mutane da yi wa mutane barazana, musamman idan ya zama ya shiga ne saboda wani babban laifi, sai ka ga yana yi wa mutane barazana da makamantan haka.

6. Karancin lafiya da lalacewar dabi’u:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next