Kurkuku Bincike Da Hukunci· Ba shi damar yin addininsa da kuma ikon saduwa da duk malami na addinin nasa. · Ba shi damar ziyartar wani makusanci nasa da ba shi da lafiya ko ya ziyarci jana’izarsa. · Kiyaye duk wani kaya da dukiya nasa. · Masu tsaron furzin dole su zama mutane ne da suke da mutunci suka kuma san mutuncin dan Adam da tausaya masa. Haka ma shugaban furzin ya zama yana da kyawawan dabi’u na gari. · Hana namiji daya shi kadai koda ma’aikaci ne shiga bangaren mata. · Kada a yi amfani da karfi a kan su sai dai idan ya zama a halin kare kai. · Kula da tarbiyya da ilimin na furzin da sauransu ta yadda kafin ya fito ya koma cikin mutane ya zama salihin mutum. Da kuma yi musu tarbiyyar da zasu ji cewa su ma mutane ne, ba wai sun fita daban daga cikin sauran mutane na waje masu hakki ba ne. · Bambancin na waje da na furzin ba komai ba ne sai a halarcin yawo kawai, amma a sauran abubuwa ba su da wani bambanci. · Sanya musu tsarin karatu da malamai kamar yadda yake a waje kuma kowanne yana iya zabar kos din da zai yi har zuwa Digiri ko Dakta. · Karfafa yawan haduwarsu da danginsu da kuma tunanin rayuwarsu ta gaba da abin da zasu zama nan gaba. Kamar yadda aka haramta tsare mahaukaci, saboda haka duk wanda ya samu hauka to dole a fitar da shi daga furzin.
|