Kurkuku Bincike Da Hukunci2. Jahilan Likitoci. 3. Mayaudara kamar ‘yan 419. 4. Mai kwacen dukiyar mutane. 5. Mai cin dukiyar marayu. 6. Mai ha’inci cikin amana daga na 5 zuwa na shida ana sayar da kayansu ne a biya idan an tsare su suka ki biya. 7. Mai taurin bashi alhali yana da shi. 8. Mai da’awar ba shi da shi alhalin ba haka ba ne, wadannan duk ana tsare su in sun ki biya har sai sun biya, kamar yadda Hakimusshar’i yana iya sayar da kayansu ya biya masu bin bashi. Mai iya aiki ya lizimta masa yin aiki domin ya biya. 9. Wanda ya ki ciyar da matarsa babu rashi. 10. Mai lamuni har sai ya zo da wanda ya lamunta ko ya biya abin da yake kansa. 11. Wanda yake da wani hakkin Allah ko na mutane akansa sai a tsare shi har sai ya zo da shi.
|