Kurkuku Bincike Da Hukunci



Amma game da kashe kashensu a kan kasa su kamar haka;

Gidan Sarka na taka tsantsan: wanda wuri ne da a kan tsare wasu wadanda ake bincike domin tsoron guduwarsu har a gama bincike. Gidan Sarka na hakkoki: wanda a kan tsare wadanda suka take hakkin Allah ko na mutane ko na kasa da makamantansu. Gidan Sarka na laifuffuka: shi ne wanda a kan tsare masu laifi a cikinsa kamar na fashi ko kisa da makamantansu.

 

CIYARWA DA KUDIN KASHEWAR FURSUNA

A wasu kasashen kudin da a kan kashe wa Gidajen Furzin ya kai kudin da a kan kashe a kan makarantun kasar kamar yadda lissafin haka ya nuna, ina ganin wannan domin ya kasance yawancin laifuffukan da ake tsarewa a kansu sun saba da sakon Allah da hukuncinsa kan masu laifuffuka.

An yi umarni da ya zama hayar Gidan Sarka (kamar yadda aka sani Gidan Sarka a musulunci kowane mutum yana da gida da a kan tsare shi koda kuwa gidansa ne) da ciyarwar na furzin tana kansa ne koda kuwa ta hanyar neman kudi ne a gidan da aka tsare shi kamar ta hanyar aiki ko kasuwanci, amma idan tsare shi da aka yi ya kai ga hana shi sana’a ko aiki ba shi da kuma wata dukiya (kamar yadda yake Musulunci bai hana na furzin sana’a ba ko tijara a gidan da aka tsare shi, kafiran da aka kamo daga Badar an yi musu tsari da ukuba da umarnin su koyar da yara goma rubutu da karatu ne, kamar yadda an raba su a gidajen musulmi ne a matsayin Gidan Kasonsu) to ya zama dole a ciyar da shi.

A wannan mas’alar akwai sabani da yawa tsakanin malamai a kan shin za a ciyar da shi ne ko kuwa? Domin wasu sun bambanta tsakanin tsaron bincike da ba a riga an tabbatar da laifinsa ba tukun da waninsa, ko tsaron har abada da na dan lokaci, da tsaron dan lokaci kankani da waninsa da makamantansu. Amma wasu littattafan sun nuna cewa matukar an tsare mutum koda yana da dukuya to ciyarwarsa zata kasance daga Baitul Mali ne, amma su ma suna sanya sharadin ya zama ba shi da dukiya tasa ta kansa ko kuma an hana shi neman dokiyar sakamakon tsare shi. Kamar yadda hayar wajan da aka tsare shi kamar gidan da yake ciki in na haya ne ko kuma Daula ta kama hayar wani gidan domin tsare shi a ciki duk yana kansa ne, domin da bukatar ya zama an sami gidan da aka tsare shi domin gudun kar ya rika fita yawo ko kuma ya gudu. Amma idan ba shi da dukiyar da zai ciyar da kansa babu kuma daga hukuma (Baitul Mali ko sadaka) ko dangi, wanda zai dauki nauyin hakan to ya zama dole a kan Daula ta sake shi domin kada ya mutu da yunwa, kamar yadda bai halatta ba a rika fito da su cikin sarka da nufin kar su gudu, ko tare da dan doka suna bara da rokon abin da zasu ci. Haka nan likkafaninsu da kudin binne su da sayan wajan da za a binne su duk suna da wannan hukuncin, domin bai halatta ba a bar shi babu salla gare shi, ba likkafani, ba binnewa, da sunan babu kudin da za a yi masa hakan.

 

HAKKIN FURSUNA A KAN SHUGABA

Akwai wasu hakkoki da tsararru suke da shi a kan Shugaba ko kuma Alkalin alkalai wanda suka hada da:

1.   Kula da halin na tsare

Dole ne shugaban musulmi ko alkalin alkalai da yawanci a wannan zamani namu da furzin yana karkashinsu ne su rika kewayawa gidajen furzin suna binciken fayel din na tsare, kuma a shelanta cewa rana kaza duk wanda yake da na tsare ya zo za a zauna da Alkalin alkalai ko Shugaban Kasa domin sanin hakikanin al’amarin na tsare, kamar yadda za a zo da na tsaren shi ma wajan zaman, idan an tabbatar da gaskiyarsa sai a sake shi idan kuma ba haka ba to sai a ci gaba da tsare shi, kuma wannan ba ya hana bayan wasu watanni ko shekara a sake duba wa ga al’amarinsa a karo na gaba.

2.   Kula da bukatun na tsare:

Ya zama dole ga shugaba ya kula da bukatun na tsare game da rayuwarsu, da abincinsu, da iskar da suke shaka, da ruwan sha caftacacce, da tufafin lokacin sanyi da na lokacin zafi, da furij, da Intanet, da talabijin da radio da jarida, da mujallu, da laburare da littattafan bincike da takardu da kayan rubutu, da kayan sana’a, da satalayet, da iya kondeshan da injin dumama daki, da injin wanke tufafi, da kompita da bidiyo da kaset da sidi ko duk wani abu da suke bukata, sai dai dole a kiyaye wasu abubuwan a tabbatar ba su yi amfani da shi ta mummunar hanya ba, kamar kallon fila filai na haram ko tasha ta haram. Kamar yadda dole ne a samar musu da filin kwallo da na sauran wasanni iri iri, da makarantu da karatu tun daga matakin Firamare har zuwa Jami’a.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next