TSari Da Kayyade Iyali6. Idan kuwa halitta ta cika (dan wata hudu) dinare dubu wato diyya cikakkiya[9]. Hukuncin Azalu
Azalu halal ne namiji ya yi shi ga mace wacce suka yi auren mutu’a da ita, haka nan ga baiwa, amma ‘ya mai aure da’imi da ba na mutu’a ba sai da izininta, in kuwa ya yi ba da izininta ba ya aikata karahiya kamar yadda natijar da aka samu kenan bayan an hada ruwayoyin da suka hana da wadanda suka halatta masa ko ba izininta. A 1- Wacce aka samu yakini ba ta haihuwa 2- Mai shekaru da yawa 3- Wacce ba ta shayar da danta in ta haihu 4- Baiwa 5- Mai karancin kunya da rashin kame kai 6- Mai zage-zage da alfahasa 7- Auren mutu’a[10] Jinkirta Yin Aure
Wannan ita ce hanya ta uku da ake amfani da ita wajan kayyade iyali ko tsara su. Wannan hanyar ma halal ce kamar yadda yake gun malamai amma ba a son ta, kamar yadda akwai ruwayoyin da suka yi nuni da mustahabbancin yin aure da wuri musamman ga mace idan ta isa aure da suke cewa; in ba haka ba fasadi yana iya faruwa a bayan kasa.
|