TSari Da Kayyade Iyali
Kame Kai Ga Barin Jima’i
Hanya ta hudu ita ce kame kai ga barin jima’i, shi ma halal ne sai dai ba a son sa a shari’a, har ma an haramta kame kai kwana arbai’in ba tare da an kusanci iyali ba kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni da cewa idan ya bar ta kwana arba’in ya yi zunubi.
Sauran Hanyoyi
Amma sauran hanyoyin da muka kawo a farkon wannan bahasi ba su da hani na shari’a sai dai kawai akwai abin da kan iya haramta su idan sun lizimci haram kamar ajnabi ya ga farjin mace ko sauran jikinta da aka haramta masa gani. Koda yake ana iya cewa su ma ba a son su ta fuskacin shari’a duk da halal ne saboda ana son yawaita al’umma idan karancinta zai kai ga lalacewar tsarin zamantakewa. Amma idan ya zama yawaitarta yana iya lalata tsarin zamantakewar al’umma a nan ya zama dole a kayyade ta.
Ra’ayin Sayyid Sadik Rauhani
A littafin fararru da sababbin mas’aloli na Sayyaid Sadik Rauhani shafi 141[11]. Bayanai game da Tsara iyali ya zo kamar haka ne: Yawaita iyali a musulunci abin nema ne da aka kwadaitar da shi amma kuma kayyade iyali halal ne, hanyoyin da a kan bi wajan kayyade iyali su ne kamar haka: -
1-Azalu.
2-Jinkirin yin aure domin kada a samu saurin tara ‘ya’ya.
3-Daina jima’i da iyali gaba daya domin gudun kada a samu ‘ya’ya.
4- Ila’i.
Kamar yadda suke su ne hanyoyi hudu da a kan yi amfani da su don kayyade iyali, koda yake akwai wasu hanyoyin daban. Ganin cewa ni’imar samuwar ‘ya’ya tana neman shiga cikin hadari ne ya sanya coci take neman hanyoyin kai wa ga sanya kayyade iyali ya zama haram. Ni’imar ‘ya’ya ta zama hadari, daga kuma matsalar karshe da malamai da masu tafiyar da al’amuran duniya suka shagaltu da ita a mafi yawan kasashe, ga kuma matsalar da ake fuskanta ta ninninkawar mazauna bayan kasa a duniya, alhalin gashi a duniya yanzu ana samun karancin mace-macen yara sakamakon maganin cututtukan yara da likitoci suka yi, ga kuma takaitawar yake-yake da sukan salwantar da rayuka masu yawa, sannan ga matsalolin da dauloli da kasashe suke ciki na kasawa da gazawa wajan maganin talaucin da yake addabar Duniyar dan Adam, amma sai ga yawan dan Adam yana karuwa mai ban tsoro da yanzu dan Adam ya kai biliyan shida a duniya a wannan zamani.
Bertrand Russell (1872-1970) yana cewa: Adadin mazaunan duniya zai kai biliyan uku da rabi nan da shekaru ishirin da biyar masu zuwa saboda haka wannan yana bukatar tunani na musmamnan kan wannan mas’ala, da farko ana ganin abin kamar mai sauki ne amma bayan lokacin kadan za a fahimci cewa matsala ce babba mai wuyar warwara.
Cocin Katolika ta yi kokarin hana kayyade iyali ta kowane hali da dukkan matakai amma ta yarda da daukar mataki na hana daukar ciki daga ma’auratayya da gangan. Wannan yana nufin ta yarda da daukar hanya ta dabi’a da al’ada domin hana daukar ciki ta hanyar tasiri kan jijiyoyi. Amma matsayin da shari’ar Musulunci mai tsarki ta dauka kan wannan shi ne, kallon abin ta mahanga biyu; wato Tsara iyali da kuma kayyade iyali.
|