TSari Da Kayyade Iyali



Ra’ayin Sayyid Sistani (A.Y.R)[12]

Amma Sayyid Sistani a risalarsa ta Minhajus-salihin[13] yana cewa ne: Ya halatta mace ta yi allurar maniyyin mijinta amma bai halatta ba mai yi mata allurar ya zama ajnabi idan wannan zai kai ga ajnabi ya ga inda bai halatta ba a gani a jikinta ko taba inda bai halatta ajnabi ya taba ba a jikin mace. Sannan ya ci gaba da kawo hukuncin kayyade da Tsara iyali yana mai cewa: ya halatta mace ta yi amfani da kwayoyin da sukan hana daukar ciki da sharadin wannan ba zai kai ga cutar da ita ba cuta mai tsanani haka yake ko da yardar mijinta ko ba da yardarsa ba.

A mas’ala ta 71 ya ci gaba da cewa: Ya halatta mace ta yi amfani da (Laulab) wato kwayar da a kan sa a mahaifa domin ta hana daukar ciki amma da kiyaye sharuddan da ka fada na hana ajnabiyyi gani ko taba abin da yake haramun ya gani ko ya taba a jikinta idan sanya shi ya tsayu a kan hakan. Kuma ba a san cewa yana iya kai wa ga barin ciki ba bayan ya zama da a mahaifa, amma idan an san zai kai ga haka to ihtiyadi wajibi a bar shi.

Haka nan ya yi magana ga yin aiki domin daina haihuwa ko yanke gabobin da sukan haifar da mani da wadancan sharuddan da kuma sharadin rashin cutar da kai.

Amma game da zubar da ciki yana cewa ne bai halatta ba sai bisa hali daya; ya zama rai bai shige shi ba kuma rashin zubar da shi zai cutar da uwar, amma idan rai ya huru a cikinsa bai halatta ta zubar da shi ba ta kowane hali.

Mahangar Sayyid Sabik

Amma Mai Fikihus-Sunna Sayyid Sabik yana kawo wa a juzu’i na biyu na littafin a shafi na 193[14] a cikin bayaninsa da na takaita shi kamar haka: Musulunci yana son yawaita iyali kuma bai hana kayyade iyali ba a bisa wasu halaye na musamman, kamar ga wanda ba ya iya tarbiyyar ‘ya’yansa tarbiyya ta gari saboda yawan iyali ko talauci, ko mace ta kasance tana da rauni, ko tana da saurin daukar ciki.

Ya ce: A irin wannan halin wasu malamai suna ganin mustahabbi ne kayyade iyali. Imam Gazali ya kara kan haka da cewa: Haka ma idan mace tana jin tsoron kyawunta kar ya tafi. Saudayawa mata suna da kyau, amma idan suka haihu daya ko biyu sai kyawunsu ya fara tafiya.

Ya ce: Wasu malamai sun tafi a kan halaccinsa ta kowane hali suna masu dogaro da hadisai a kan haka. Kamar yadda yake a ra’ayin Shafi’I, da Al-baihaki, da Sa’ad Dan Abi Wakkas, da Abi Ayyubal Ansari, da Zaidu Dan Sabit, da Dan Abbas (R.A) kuma shi ne mazhabar Maliki, da Shafi’i.  Ya ce: Ahluz-zahir ma’abota zahiri suna ganin haramcin kayyade iyali da hana azalu suna masu dogaro da wasu hadisai.

Kayyade Iyali A Kiristanci

Amma Dakta Ahmad Asshalbi a littafinsa Mukaranatul Adyan juz’i na biyu shafi na 202 yana cewa[15]:

Kiristoci suna himmantuwa da yawaita haihuwa suna kuma gaba da kayyade iyali, daga cikin abin da aka danganta ga Alibaba Biyus na goma sha biyu a kungiyar iyali ta kasar Italiya shi ne:

Lallai yawaita iyali shi ne sharadin aminci ga al’ummar kirista kuma dalili ne a kan imani da Allah da aminta da taimakon Allah kuma yana sanya farin cikin iyali, kiristoci suna dada bayar da muhimmancin yawaita iyali a kasashen da suke ‘yan kadan ko kuma suke daidai da sauran ‘yan kasar wanda ba kirista ba, shi ya sa ma a gabas musumman suke da shaukin yawaita al’umma a daidai lokacin da wasunsu suke kokarin ganin sun kayyade iyali ko tsarawa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next