TSari Da Kayyade IyaliMuna iya cewa; Kiristanci Addini ne da yake da karancin hukunce-hukunce kuma yake himmantuwa da tsarkake kai, ba ya himmantuwa da al’amuran duniya, kamar yadda yake ciko ga addinan ‘ya’yan Isra’ila, shi ya sa suka bar mafi yawan shari’a ko ma dukkanta suka fuskanci bangaren zuhudu da soyayya da rangwame. Mahangar Salih Al-Wirdani
Amma Salih Al-wirdani a littafinsa na Asshi’a Fi Misra a shafi na 197 yana fada cewa[16]: Ba ya halatta zubar da ciki a kowane lokaci matukar ya shiga, mace tana iya amfani da duk abin da zai iya hana ta daukar ciki, idan ba zata iya tarbiyyar ‘ya’yanta ba, ba abin da zai hana ta kayyade iyali da yanke haihuwa. Mahangar Bakir Sharif Al-Kurshi
Amma Bakir Sharif Al-kurshi a littafinsa na Tsarin Siyasa a musulunci a shafi na 246 yana kawo tsarin tafiyar da al’amura a musulunci ne, zamu yi kokarin kawo wasu daga cikinsu a nan saboda ya shafi abin da muke magana a kai ta wani bangare[17]. Ya ce: Abubuwan da daular musulunci ta ginu a kansu na siyasarta ta cikin gida su ne: 1. Tsayar da adalci 2. Kawar da talauci A cikin wannan a bayanansa ya kawo cewa malaman tattalin arziki sun tafi a Ya ce: Ikbal yana cewa: Bincikena bayan na karanta shari’ar musulunci karatu mai zurfi mai tsawo ya kai ga cewa; duk inda aka fahimci wannan shari’a fahimta mai kyau kuma aka aikata ta kamar yadda ya kamata to hakkin rayuwa zai zama mai sauki ga kowa. Ya ce: Matsalar burodin ci tana dada ci gaba, sai dai da dacewar Allah mun sami warwara a cikin shari’ar musulunci da hukunce-hukuncenta. Ya ci gaba da cewa: Zai nuni da wasu daga cikin hanyoyin dalla-dalla: 1. Aiki tukuru domin samar da kayan masarufi, daga abubuwan da
|