Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Kamar yadda yake haduwar malamai a kan wani hukunci yana nuna ingancin wannan hukunci a shari’a haka nan haduwar dukkan musulmi a kan wani aiki yana nuna mafi daukaka kasantuwan wannan abin a cikin shari’a.[4]

 

Masu Haramta Tafiya Don Ziyarar Manzo

 Har zuwa karshen karni na bakwai malamai sun hadu a kan wannan al’amari cewa tafiya domin aiwatar da wani aiki na mustahabbi koda ba ta zama mustahabbi ba to alal akalla ta halasta. Amma a farkon karni na takwas, Sai Ibn Taimiyya ya yi riko da hadisin Manzo wanda Abu Huraira ya ruwaito ta yadda ya saba wa dukkan malamai da suka hadu a kan wannan al’amari. Wannan ruwaya kuwa da Ibn taimiyya ya yi mafani da ita, an ruwaito ta ne ta fuska guda uku, amma abin da yake iya tabbatar wa Ibn taimiyya da manufarsa ya zo da fuska biyu ne kamar haka:

1- Kada a yi nufin tafiya sai zuwa masallatai guda uku: Wannan masallaci nawa, masallacin ka’aba da Masallacin Kudus.[5]

2- Ana yin tafiya ne kawai zuwa ga masallatai guda uku[6], Ibn taimiyya ya yi riko ne da zahirin wannan hadisi domin tabbatar da manufarsa, ta yadda ya yi da’awar cewa domin aiwatar da ayyukan ibada masallatai uku ne kawai mutum zai iya zuwa domin yin hakan. Saboda haka ziyarar Manzo wanda yake matsayin ibada ba ya daya daga cikin wadannan abubuwa guda uku. Wannan kafa hujja ta Ibn Taimiyya kuwa idan muka lura da kyau zamu iya gane rashin ingancinsa, domin kuwa ba shi da kafafu masu karfi.

 Domin kuwa mun san cewa jumlar da take kebewa tana ginuwa daga sassa guda biyu kamar haka:

1-Jumlar da ake kebewa daga gareta: "Ba wanda ya zo wurina".

2- Jumlar da a ka kebance "Sai Ali"

Hadisin da ya gabata ya ginu ne ta hanyar jumloli biyu ne:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next