Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Kamar yadda wasu ba su ba wannan bayani muhimmanci ba, (mu dauka ma wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu) kafa hujja da shi a kan rusa gine-ginen da aka yi a kaburburan bayin Allah, zai fuskanci matsaloli guda biyu:

 1-Baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu ya sabawa dukkan ra’ayin fukaha domin kuwa dukkansu sun tafi a kan haka din cewa mafi karanci tashinsa ya kai kamun hannu guda.[46]

 2-Idan muka dauka cewa wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daidai da kasa, to dole ne mu rusa kabari ta yadda zai zama daya da kasa, ba wani gini da aka yi ba a saman kabarin. Saboda haka sam wannan hadisi ba yana magana ba ne a kan ginin da yake kan kabari yana magana ne a kan shi kansa kabarin!.

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yi umarni da girmama annabawa da wasiyyansu.


[1] -Wasu daga cikin malamai sun ata fi a kan cewa duk abin da yake gabatrwa ne domin aiwatar da abin yake mustahabbi ne to shima wannan abin mustahabbi ne. sannan suna kafa hujja ne da wadannan ayoyin kamar haka: Nisa: 100, Tauba: 120-21.

[2]-Ibn Asakir: Mukhtasari tarikhi damashk, 5: 265, Tahzibul kamal: 4289.

[3] Subki: Shifa’us Sikam: 143.

[4] -Shifa’us sikam: 1001-101.

[5] Sahih Muslim: 4: 126. Duk da yake cewa, wannan hadisi ba ya tabbatar da manufar Ibn taimiyya, domin kuwa umurni a kan ziyarar wadannan masallatai guda uku ba nuna haramcin ziyar waninsu.

[6]-Sahih Muslim. Kamar na sama.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next