Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)A unguwar Bani Hashim a garin Madina shekaru kadan da suka gabata gidan Imam Hasan da Husain (A.S) da makarantar Imam Sadik (A.S) sun kasance a wadannan wurare, Marubucin wannan littafi shi kansa ya ziyarci wadannan wurare, amma abin bakin ciki tare da fakewa da fadada masallacin Manzo duk an rusa wadannan wurare masu dimbin tarihi da albarka. Duk da cewa ana iya yin wannan aiki na fadada masallacin Manzo (S.A.W) ba tare da rusa wadannan wurare ba.
Soyayyar Manzo (S.A.W) Da Iyalansa Ayoyi da hadisai da dama sun zo domin bayani a kan soyayya ga Manzo da ‘yan gidansa (A.S). Kur’ani ya nuna mana cewa imanin abin ceta shi ne ya kasance yana tare da wanda yake son Manzo da jihadi a tafarkin Allah fiye da komai a cikin zuciyarsa: "Ka ce idan iyayenku da ‘ya’yanku da matanku da ‘yan’uwanku da dukiyoyinku wadda kuka tara, da kasuwanci da kuke tsoran ku fadi a cikinsa, da gidajenku da kuke kaunarsu, idan sun kasance sun fi soyuwa a gareku daga Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah sai ku saurara har al’amarin Allah ya zo, Allah ba ya shiryar da mutane fasikai".[23] Ayar sama tana magana ne a kan abubuwa guda uku wadanda mafi yawa soyayyar mutum takan ta’allaka da su, wato Iyalai da dukiya da gidaje da saye da sayarwa. Amma mumini na hakika shi ne wanda Allah da mazonsa da jihadi a tafarkin Allah ya fi soyuwa a gare shi fiye da wadancan abubuwa da aka ambata. Amma a wata aya ana bayani ne a kan soyayyar iyalan gidan Manzo ga abin da take cewa: "Ka ce ban nemi wani abu a kan sakon manzancin da na zo da shi ba a matsayin lada sai soyayya ga iyalan gidana". [24] Sannan Manzo yana bayyana wasu abubuwa guda uku wadanda suke nuna dandana zakin imanin mutum, daya daga cikinsu shi ne soyayya ga Allah da shi manzon: Abubuwa guda uku ne duk wanda yake da su to ya dandana zakin imani, daya daga cikinsu kuwa shi ne ya kasance a wajan mutum son Allah da manzonsa ya fi komai a wajensa… Ruwayoyi da suka zo dangane da son Manzo da iyalansa sun wuce gaban mu kawo su a cikin wannan littafi, saboda haka a nan zamu takaia da wasu ruwayoyi a matsayin misali dangane da wannan al’amari, muhimmin abu a nan shi ne mu san ta yaya wannan soyayya zata tabbata, domin mutum ya isa zuwa ga wannan hadafi akwai hanyoyi guda biyu: 1-Mutum ta hanyar magana da ayyukansa ya yi koyi da koyarwar Allah da manzonsa, ta yadda zai kasance a rayuwa ya yi kokari ya ga bai kauce wa koyarwarsu ba, domin kuwa idan mutum ya zamana yana tsananin soyayya ga wani ba zai taba saba masa ba. Saboda haka ne ake cewa "soyayya ita ce biyayya". Wato sonka da abu yana lizimta maka da yi masa biyayya.
|