Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W) Tare da kula da wannan ma’ana ta kalamar bait, fassara ta da ma’anar masallaci yana bukatar abin da yake nuna hakan, ba tare da wannan ba ba za a karbi wannan fassara ba. 2-Kur’ani duk lokacin da zai yi magana a kan wurin da al’umma suke bauta yana amfani ne da kalmar "masjid" ko "Masajid" ne. Sakamakon haka ne wannan kalma an yi amfani da ita sau 28 acikin Kur’ani mai girma. Amma duk lokacin da za a yi nagana a kan wurin da mutane suke kwana a kan yi amfani da kalmar "Maskan, Ma’awa" ne. Sannan an yi amfani da kalmar bait ta fuskar jam’i ko tilo. Saboda haka wannan kalma ta zo sau 66 a cikin Kur’ani da wannan manufa, sakamakon haka muna iya fahimata cewa a cikin Kur’ani kalmar "Masjid" da "bait" ba suna nufin ma’ana guda ba ne. saboda haka idan aka nemi fassara su da ma’ana guda zai zama da’awa ba tare da dalili ba. Idan Kur’ani ya kira masallacin Ka’aba da "baitullahi"[13] ba don yana wurin bautar Allah ba ne, domin kuwa mun san cewa Ka’aba alkibla ce ta masu bautar Allah ba wurin da ake ibada ba. Saboda haka hada sunan Allah da wannan wurin kawai yana nuna girmamawa ne, kai ka ce wannan gida na Allah ta yadda za a girmama shi girmamawa ta musamman. 3-Akwai muhimmin bambanci tsakanin masallaci da gida, Bait ana nufin bangaye guda hudu da aka yi wa rufi, amma masjid kawai bangaye guda hudu ne, wato rufi ba sharadi ba ne kafin ya zama masallaci. Da yawan akan gina masallatai a wuraren da suke da zafi ba tare da rufi ba, wanda daya daga cikinsu shi ne masallacin ka’aba, alhalin kuwa gidan da mutum yake kwana yana bukatar rufi. Wannan aya da zata zo a kasa tana bayar da sheda a kan bukatar gida daga rufi: "Ba don hikimar Allah ta yi rigaye ba akan cewa komai zai kasance bai daya, da mun sanya gidajen wadanda suka kafirce wa Ubangiji mai rahama masu rufi da azurfa da tsanin da suke amfani zuwa sama".[14] Wannan aya tana bayyana cewa "bait" sabanin "Masjid" yana da rufi, sannan ba don wata maslaha ba da Allah madaukaki ya bambanta gidajen kafirai da na muminai ta yadda zai sanya gidajen Kafirai rufinsu ya zama na azurfa, amma sai bai yi hakan ba. 4-Jalaluddin Suyudi ya ruwaito daga Anas bn Malik Yana cewa: Yayin wannan aya wadda take cewa "A cikin gidajen da Allah ya yi Umarni da a daukaka….". Sai ya karanta a cikin masallaci, sai wani daga cikin sahabban Manzo ya mike ya tambayi Manzo me ake nufi da wadannan gidaje? Sai Manzo ya amsa masa da cewa: Ana nufin gidajen Annabawa, a wannan lokaci sai Abubakar ya mike ya ce: Ya nuna gidan Ali da Fatima (A.S) ya ce wadannan gidajen suna cikin wadanda Allah ya yi izini da daukaka su?. Sai Manzo (S.A.W). ya amsa masa da cewa: E, suna ma daga cikin mafi daukakarsu.[15] Imam Bakir (A.S) yana cewa: Abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya shi ne, gidajen Annabawa da gidan Ali (A.S)[16]
|