Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W) Ibn Jubair ya ambaci wani wuri da ake kira "Karafa" inda yake cewa yana daga cikin wurare masu ban al’ajabi kamar yadda ya bayyana akwai kaburburan annabawa da iyalan Manzo da sahabbansa da tabi’ai da sauran kaburburan manyan malamai da aka rufe a wannan wuri. Dan Annabi Salih (Raubil) dan Annabi Yakub (Ishak) da matar Fir’auna dukkansu an rufe su ne a wannan wuri. Haka nan daga cikin iyalan Manzo akwai dan Imam Ja’afar mai suna kasim da dansa Abdullah bn Kasim da dansa Yahya bn Kasim, sannan da kabarin Ali bn Kasim bn Abdullah bn Kasim da dan’uwansa Isa bn Abdullah. Ibn Jubair ya ambaci da yawa daga cikin ‘ya’yan Ali (A.S) wadanda aka rufe su a can. Haka nan akwai kaburburan Sahabbai tabi’ai ba shugabanni kamar Imam Shafi’i ta yadda yake magana a kan girma da matsayin haraminsa, kamar yadda yake cewa: Salahuddin Al’ayubi shi yake biyan kudin da ake bukata domin gabatar da bukukuwa a wannan harami na Imam Shafi’i.
Hasumiyoyi Masu Tsawo A Garin Makka Ibn Jubair yana bayyana yadda garin Makka ya kasance da hasumiyoyi masu daukaka a kan kaburbura a garin Makka, wanda ambatonsu a nan zai janyo mu tsawaitawa. Akwai wurare kamar Maulidin Nabi, Maulidin Zahara da Darul Khaizaran (wurin ibadar Manzo na sirri). Sannan ya ambaci wurare masu girma na sahabbai da tabi’ai a Madina, A cikin wannan kuma yake ambatar Raudhar Abbas bn Ali bn Hasan bn Ali (A.S) wanda yake da gini mai tsayi a garin Madina, sannan ya cigaba da bayyana yadda wadannan wurare suke. Idan muna so mu fadi duk abubuwan da Ibn Jubair ya gani a garuruwan Sham da Iraki na sahabbai da manyan bayin Allah zai janyo mu tsawaita a cikin hakan. Don haka muna iya wadatuwa da wannan. Saboda haka wanda yake so ya samu karin bayani sosai a kan haka sai ya koma zuwa ga wannan littafi nasa.[30] IBn Najjar (578-643) [31] Muhammad bn Mahmud wanda aka fi sani da Ibn Najjar wanda yake shi ma shahararren musulmi mai yawon shakatawa ne a cikin littafinsa "Madinatur Rasul" yana cewa:
|