Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W) Sannan Imam Sadik (A.S) a wasu baituka yana bayyana bambanci tsakanin soyayya ta gaskiya da nuna soyayya da ba ta hakika ba, Inda yake bayani akan cewa: Kana sabon Allah alhali kana nuna soyayya gare shi, Wannan ba zai taba yiwuwa ba, Domin da sonka ya kasance a gaskinya ne, to da ka yi biyayya a gare shi, Domin kuwa masoyi yana bin abin da abin so yake so. [25] 2-Bayyana soyayya ta hanyoyi daban-daban kamar haka: A- Nuna farin cikin yayin da masoyi yake cikin farin ciki, da nuna bakin ciki yayin da masoyi yake cikin bakin ciki; B-Gabatar da buki na farin cikin a lokacin haiwuwar Manzo ko lokacin tayar da shi a matsayin ma’aiki; C-Yada maganganunsa da abin da ya rubuta; D-Kiyaye kayan tarihin da suka shafe shi;
|