Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



Domin Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)

 Ziyarar Kabarin dukkan musulmi da musamman ziyarar kabarin Manzo wani abu ne wanda yake mustahabbi mai karfi a cikin musulunci. Sannan malaman hadisi daga Sunna da Shi’a sun ruwaito hadisai da dama a kan mustahabbancin ziyarar kabarin Manzo wadanda wasu daga cikinsu sun gabata a cikin bahasin da ya gabata ta yadda babu wani malami daga cikin malaman musuluncin da ya ba kansa damar yin shakku a kan mustahabbancin ziyarar Manzo. Wannan kuwa ya hada har da Muhammad bn Abduh wanda yake da wasu masatlolin dangane da abin da ya shafi annabawa, a nan ba kawai ya yi shiru ba ne, sai dai ya yi magana a kan mustahabbcin ziyarar Manzo (S.A.W). Sannan mun kawo abin da yake cewa dangane da hakan a bahasimmu na baya.

 Tare da la’akari da kasantuwar mustahabbicn ziyarar Manzo, amma msulmi sun kasu a kan wannan kyauta ta ubangiji:

1-Mazauna Madina

Mazauna Madina sakamakon makwautaka da suke da ita da Manzo (S.A.W). Suna iya ziyartarsa ba tare wata wahala ba don aiwatar da wannan mustahabbi.

2-Mazauna sauran wurare a cikin duniya

Mazauna sauran sassan duniya dole ne su yi tafiya domin su damar yin sallama ga kabarin Manzo Su ce: "Amincin Allah ya tabbata a gareka ya manzon Allah".

 A nan tambaya ita ce; menene hukuncin wannan tafiya a shari’a?

Jawabain wannan tambaya kuwa a fili yake domin wannan amsa tana matsayin gabatarwa ce domin aiwatar da aikin mustahabbi, saboda haka a akidar wasu malamai tana matsayin mustahabbi, wasu kuwa suna cewa tana hukuncin halal "Mubah" ne.

Duk yadda ta kama kasantuwar wannan tafiya domin aiwatar da mustahabbanci ce ba zata taba zama haramun ba. Domin kuwa ba zai inganta ba a hankali Allah madaukaki ya umurce mu da aikin mustahabbi na ziyartar Manzo sannan ya haramta abin da yake matsayin gabatarwa ne domin aiwatar da wannan aikin. Saboda haka daga nan muna iya gane cewa hukuncin wannan tafiya domin aiwatar da wannan aiki ta halitta. [1]



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next