Karfafa Ginin Al'umma



Na farkonta wanda za a shawartan ya kasance mai hankali.

Na biyu ya kasance da (ba bawa ba) kuma ma’abucin addini.

Na uku ya kasance aboki mai gaskiya tamkar dan’uwa.

Na hudu ya kasance saninsa ga sirrinka tamkar saninka ne ga kanka, sannan kuma ya kula da kiyaye shi.

Saboda inda ya kasance mai hankali ne za ka amfana da shawararsa, idan kuma ya kasance ‘yantacce mai addini zai ba da kokari wajen yi maka nasiha, idan kuwa ya kasance aboki mai gaskiya tamkar dan’uwa to zai rufe maka asirinka idan har ka gaya masa, idan kuwa ka gaya masa sirrinka to masaniyarsa kan hakan tamkar masaniyarka ne, (idan na samu haka) to shawara ta cika kuma nasiha ta kammala[42]”.

e) – Daga Abil Hasan al-Ridha (a.s) daga Iyayensa daga Ali (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ya Ali, kada ka nemi shawarar matsoraci, don zai kankanta maka mafita, kada ka shawarci marowaci, don zai gaza wajen (taimaka) maka isa ga manufarka, kada ka shawarci mahandami da son kai, don zai kawata maka sharrinta. Ka fa sani cewa tsoro, rowa da handama da son kai wasu abubuwa ne da mummunan zato ke haifar da su[43]”.

f) – Abu Abdullah (a.s) ya gaya wa Ammar al-Sabati cewa: “Ya Ammar! Idan kana son ni’ima ta zauna maka, sannan ka samu cikan mutumci kuma rayuwa ta yi maka kyau, to kada ka sanya bayi da kaskantattun mutane cikin lamurranka, don kuwa idan ka amince musu za su ha’ince ka, idan suka maka zance za su maka karya, idan wani bala'i ya fada maka za su guje ka, idan kuwa suka maka alkawari za su saba maka[44]”.

g) – Daga Ja’afar bn Muhammad al-Sadik (a.s) daga Iyayensa (a.s) cikin wasiyyar Manzon Allah (s.a.w.a) ga Ali (a.s) yana cewa: “Ya Ali! Mata ba su da….” har inda yake cewa: “ba sa zama alkalai kuma ba a neman shawararsu. Ya Ali! Mummunan dabi’a rashin sa’a ne, biyayya ga mace kuwa nadama ce. Ya Ali! Idan har akwai rashin sa’acikin wani abu to yana cikin harshen mace ne[45].

A wata ruwayar kuma da ke da ingantaccen isnadi daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ambaci mata sai ya ce: “ku yi musu umarni da alheri kafin su yi muku umarni da munkari (abin ki), ku nemi tsarin Allah daga ashararansu, kuma ku yi hankali da zababbun cikinsu[46]”.

WajibanMai Ba Da Shawara

A mahanga ta daban kuma kan batun da muke yi, yana da kyau mu san cewa ya zama wajibi ga mai ba da shawarar ya kasance mai nasiha yayin ba da shawara da kuma ba da kokari wajen ganin an isa ga hakika da kuma manufa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next