Karfafa Ginin Al'umma



3-     Hankali da masaniya.

4-     Kula da kuma kiyaye sirri.

5-     Daidaito cikin dabi’u, ta yadda ba zai kasance yana da wata dabi’a da za ta iya haifar da gibi cikin shaksiyyar mutum ba, kamar rowa, ragwantaka koro da sauransu.

6-     Daukaka a ido al’umma, bai kamata mutum ya nemi shawarar wulakantacce ko kuma bawa ba.

7-     Daidaito cikin yanayi da tausayi, bai kamata a nemi shawarar ma’abuta tsananin tausayi[38].

A nan, bari mu yi ishara ga wasu nassosi da za mu iya amfani da su a wannan bangare, bugu da kari kan wadanda suka gabata:

a) – An ruwaito Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Ku nemi shawarar mutanen da suke tsoron Ubangijinsu cikin al’amurranku[39]”.

b) – Daga Ali (a.s) yana cewa: “Ka nemi shawarar mutanen da ke tsoron Allah cikin maganganunka[40]”.

c) – Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Me ke hana daya daga cikinku neman shawarar mutum ma’abucin hankali, mai addini da tsantsaini idan wani abin da ya shiga masa duhu ya bijiro masa”, daga nan sai ya ce: “Lalle idan da zai aikata haka, Allah ba zai yi watsi da shi ba face dai zai daga shi, da sanya shi kan lamarin da alheri ke tattare da shi kuma wanda ya fi kusanci da Allah[41]”.

d) – Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Neman shawara ba za ta kasance ba sai bisa iyakokinta, wanda ya santa da iyakokinta, idan kuwa ba baka ba to cutarwarta ga neman shawarar ta fi amfaninta yawa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next