Karfafa Ginin Al'umma



Kai hatta shari’a ma dai ta dauki mataki mai muhimmancin gaske kan wannan batu, daga ciki har da halalcin yin karya a wajen sasantawa, da kuma rashin halalcin fadin gaskiya a wajen lalata tsakanin muminai.

Duk da cewa karya na daga cikin manyan ababen da aka haramta, amma duk da haka a wannan bangare ya kan iya zama halal karkashin iyakokin shari’a kamar yadda malaman fikihu suka ambata yayin sasantawa tsakanin mutane biyu da kawo karshen rikici.

Daga Ja’afar bn Muhammad daga Iyayensa (a.s), daga Manzon Allah (s.a.w.a): “karya ta kan halalta a wajaje uku: makida yayin yaki,…., da sasantawa tsakanin mutane. Sannan a wasu ukun kuma gaskiya ta kan zama abin ki: annamimanci, ba da labari ga wani mutum kan iyalansa na daga abubuwan da yake ki, da kuma karyata wani mutum da gangan….[19]”.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Zance uku ne: gaskiya, karya da sasantawa tsakanin mutane”, sai aka ce masa, Ya shugabana, mene ne sasantawa tsakanin mutane?, sai ya ce: “ka ji wani kalami mai muni kan wani mutum, amma lokacin da kazo gaya masa sai ka ce masa: na ji wane yana fadin alheri dangane da kai, wato sabanin abin da ka ji[20]”.

Makwabtada Karfafa Ginin Zamantakewa

Na Biyar: Kula da makwabta da kyautata alaka ta makwabtaka kamar yadda muka ambata cikin iyakokin akala ta musamman. Wannan lamari yana a matsayin aiki mai muhimmanci na musamman wajen karfafa ginin alakar zamantakewa, saboda alaka ta makwabtaka tana a matsayin alaka ta dabi’a wacce ke da muhimmanci baya ga alaka ta nasaba. A duk lokacin da alakar da ke tsakanin mutanen da ke zaune a yanki guda ta yi kyau, za a samu damar tabbatar da karuwar jin dadi, tabbatuwa da kuma tsaro ga al’ummar a yanayi na gaba daya.

Dukkan wani nassi da bayani da shari’a ta zo da su a wannan bangare zai iya shiga cikin wannan bahasi da muke yi na makwabtaka, kamar yadda a nan gaba za mu yi ishara da shi yayin da muke magana kan alaka ta musamman.

Tsare-TsareNa Aikace:

Na Shida: akwai wasu tsare-tsare na aikace da aka tsara don karfafa alakoki, daga ciki akwai:

a) – Nesantar nuna adawa da kiyayya ga mutane.

An ruwaito Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Da wuya Jibrilu ya zo wajena face sai ya ce: Ya Muhammadu! Ka ji tsoron kiyayyar mutane da adawarsu[21]”.

Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Jibrilu bai taba zuwa wajena ba face sai ya yi min wa’azi, maganarsa ta karshe gare ni (ita ce): ina gargadinka da ….., saboda tana bayyanar da sirri da kuma kawar da izza[22]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next