Karfafa Ginin Al'umma



NEMAN SHAWARA, IYAKA DA KUMA SAKAMAKONTA

A karshen bayanin da muke yi kan abubuwan da suke karfafa ginin alaka ta zamantakewa, yana da kyau mu dan yi karin bayani ko da kadan ne kan shawara, hukumce-hukumcenta, iyakokinta da kuma tasirin da take da shi, bisa la’akari da kasantuwarta daya daga cikin muhimman abubuwan da ke karfafa ginin alaka ta zamantakewa, kamar yadda muka yi nuni da hakan a baya.

Kamar yadda kuma take a matsayin abu mai muhimmanci cikin alaka ta zamantakewa.

Muhimmancin Shawara (Shura)

Musulunci da Ahlulbaiti (a.s) sun ba da muhimmancin na musamman ga batun shura (shawara tsakanin mutane), ta yadda muna iya cewa: ra’ayin Ahlulbaiti (a.s) kan nazariyyar hukumci a mataki na zartarwa, ta ginu a kan tsarin shura[28], amma a bisa matakin alaka ta zamantakewa ta gaba daya, za mu ga Ahlulbaiti (a.s) suna jaddada muhimmancin neman shawara.

Al-Barki cikin al-Mahasin ya ruwaito daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: neman shawarar mutum mai hankali shiriya ce kana kuma dacewa ce daga Allah. Ina gargadinka da kada ka saba wa shawarar da mutum mai hankali ya ba ka, saboda akwai cutarwa cikin hakan[29]”.

A wata ruwayar ta daban ta al-Barkin, daga Abi Ja’afar al-Bakir (a.s) yana cewa: “Cikin Attaura amakokwai wasu sadarori guda hudu da ke cewa: duk wanda ba ya shawara zai yi nadama, fakirci mutuwa ce mafi girma, kamar yadda ka yi haka za a maka (abin da ka shuka shi za ka girba), wanda ya mallaki (abu) shi ya fi cancantarsa[30]”.

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Neman shawara ita ce asalin shiriya[31]”.

Don sanin muhimmancin shura, yana da kyau mu yi dubi ga wadannan abubuwa cikin neman shawarar da Ahlulbaiti (a.s) suka yi ishara gare ta:

Karfida Tai

Na Farko: Shura tana daga cikin mafi girma da daukakan taimako ga dan’Adam wajen ayyuka da makomarsa, don haka shura ta zamanto karfi na hakika a alaka ta zamantakewa.

An ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa daga cikin wasiyyar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi wa Amirul Muminina Ali (a.s) har da cewa: “babu karfafaffen taimakon da yafi shawara, sannan kuma babu hankalin da ya wuce tunani[32]”.

Kamar yadda kuma aka jaddada wannan ma’ana cikin Nahjul Balaga, yayin da Amirul Muminina (a.s) yake cewa: “Babu wadatar da ta wuce hankali, babu talauci kamar jahilci, babu abin gadon da ya wuce kyautata dabi’u, haka nan babu mataimakin da ya wuce (neman) shawara[33]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next