Karfafa Ginin Al'umma



Alkur’ani mai girma ya siffanta wasu jama’a na mutanen kirki daga sahabban Ma’aiki (s.a.w.a) da cewa su “masu rahama ne a tsakankaninsu” da kuma cewa su “masu kankantar da kai ga muminai”  kuma “muminai maza da muminai mata majibintar al’amurran junansu ne”. A baya a wurare daban-daban mun yi nuni da wannan batu.

A cikin littafin al-Wasa’il akwai babi na musamman kan wannan tafarki, bari mu kawo wasu daga cikin nassosinsa.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Yana da kyau ga mumini da ya dage wajen ci gaba (da abin da yake kai), da taimako wajen tausayin juna, taimakawa mabukata, da tausayi tsakankanin juna har ku kasance kamar yadda Allah Ya umarce ku, wato masu rahama a tsakankaninsu, masu kokarin amfanuwa da abin da ya kubuce musu na daga abubuwan da Ansar suka kasance a kai a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a)[13]”.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Allah Ya yi rahama ga mutumin da ya shirya tsakanin mabiyanmu biyu. Ya ku muminai! Ku shirya tsakaninku da kuma jin tausayin juna[14]”.

SasantaTsakani

Na Hudu: Shu’urin jin sasanta tsakani, ta yadda hakan ya fi dukkan salla da azumi, saboda akwai hadisai da dama da aka ruwaito da suke magana kan falala da muhimmancin wannan aiki saboda irin tasirin da yake da shi wajen karfafa alakar zamantakewa tsakanin mutane, da kuma kawar da shinge da dukkanin matsaloli.

Malaman fikihu sun kebance babi guda kan sulhu inda suka kawo hadisai da hukumce-hukumcen da ya shafe shi.

A cikin wani ingantaccen hadisin da aka ruwaito daga Imam Amirul Muminina (a.s) (a.s) da kuma Imam Sadik (a.s) suna cewa: “Sulhunta tsakanin mutane biyu shi yafi soyuwa a gare ni kan yin sadaka da dinare biyu[15]”.

Kuma daga gare shi (a.s) yana cewa: “Kyautata tsakanin mutanen da ke fada tsakaninsu sadaka ce da Allah ke kauna, da kuma kusanta tsakaninsu idan sun nesanci juna[16]”.

Kamar yadda kuma aka ruwaito Amirul Muminina (a.s) cikin wasiyyar da ya yi wa ‘ya’yansa Hasan da Husain (a.s) bayan da Ibn Muljam ya sare shi da takobi yana cewa: “Don na ji kakanku (Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: kyautata tsakani ya fi salla da azumi[17]”.

Daga Abi Hanifa Sa’ik al-Hajj yana cewa: “wata rana al-Mufadhal ya wuce ni tare da sirikina muna fada kan gado, sai ya tsaya a wajenmu na sa’a guda ya ce: Ku zo gidana, sai muka tafi ya sasanta mu da dirhami dari hudu, ya biya wadannan kudade daga aljihunsa, har lokacin da kowani guda daga cikinmu ya amince da dan’uwansa, sai ya ce: wannan dukiya dai ba tawa ba ce, face dai Abu Abdullah (a.s) ne ya umarce ni da in sasanta mutanenmu idan har na ga suna rikici kan wani abu[18]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next