Halayen Sayyida Zahara (s.a)



Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana yi mata lakabi da "shugabar matan talikai" kuma ya yi mata alkunya da "babar babanta" yana son ta so mai tsanani, kuma yana girmama ta girmamawa mai girma, har ya kasance idan ta shiga wajansa sai ya yi maraba da ita ya mike tsaye domin girmama wa gareta, sannan kuma ya zaunar da ita wurinsa, wani lokaci har ya sumbanci hannunta, kuma ya kasance yana cewa: Allah yana yarda da yardar Fadima yana kuma fushi da fushinta[14].

Ta haifa wa Imam Ali (a.s) Imam Hasan da Imam Husain da Muhsin (a.s) wanda aka yi barinsa saboda cutarwa da babarsa ta fuskanta, da kuma sayyida Zainab, da Ummu kulsum (a.s).

Wafatin Nana Fatima (a.s): Kamar yadda muka san ice cewa sayyida Zahara (a.s) ta samu kantaa cikin wani hali na bakin cikin rabuwa da Mahaifinta, ta yadda kullum tana cikin kuka da bakin ciki. ta yadda ba za ta iya kamewa ba, wannan hakika yana faruwa ne saboda abu uku:-

ط¢آ·        Ta fi kowa sanin matsayi da darajar Mahaitinta, muhimmancin rayuwarsa cikin al'umma da abin da wafatinsa ya kunsa na rashi cikin wannan afumma.

ط¢آ·        Abubuwan da za su sami zuriyarta a baya na kisa da dauri a daidai lokacin da kowa ya juya musu baya, ba su da wani mai taimako sai Allah.

ط¢آ·        Fitintunu da bala'i da al'ummar musulmi za su dinga shiga. sakamakon barin wasiyyar manzo ta biyayya ga Imam Aliyu ((a.s)) da sabawa wasiyyar Manzo (s.a.w). ta yadda shugabancin musulmi zai koma hannun jabbirai  mashaya giya da sunan khalifancin Mahaifinta bayan wasu lokuta kamar yadda ya faru a daulolin Banu Umayya da Banu Abbas

Ba ka jin komai sai kuka cikin gidan Imam Ali (a.s), mutanen Madina ko'ina sai kuka kake ji. Matan Banu Hashim dukkansu sun hadu cikin gidan suna ta kuka. Imam Aliyu ((a.s)) yana zaune a tare da shi akwai Hasan da Husaini, suna ta kukan rabuwa da mahifiyarsu. Ita kutna Ummi Khulsum ta fita waje tana kuka tana cewa: "Ya Babanmu, Ya Manzon Allah, hakika yau kam mun rasa ka dukkannin rasawa, babu saduwa nan duniya har abada, mutane kuwa sai zuwa suke ba iyaka suna yi wa Imam Aliyu ((a.s)) ta'aziyya.

Sai Abubakar da Umar suka ce: In za a yi mata salla a bari sai sun zo ko kuma a aika musu. Nana (a.s) ta yi wafati ne bayan la'asar zuwa magriba, lokacin da jama'a suka ga dare ya yi ba a yi mata salla ba, sai suka yi zaton jana'izar sai gobe za a yi, don haka sai suka watse. sai wadanda aka sanar da su yadda abin yake kawai suka tsaya. Cikin wannan daren Imam ((a.s)) ya yi mata wanka, Asma'u tana zuba mishi ruwa, sannan ya sanya mata likkafaninta. Lokacin da dare ya yi nisa sosai mutane sun yi barci. sai Imam ya kira jama'arsa suka yi wa Nana ((a.s)) salla. wanda suka hada da: Salmanul Farisi. Ammar Ibn Yassir. Abu Zarri Gifari. Mikdad. Huzaifatul Yamani. Abdullahi Ibn Mas'ud. Abbas Ibn Abdulmuttallib. Fadeel Ibn Abbas. Akilu. Zabair Ibn Ayywam, Buraida da wadansu 'yan jama'a daga Banu Hashim.

Imam Ali (a.s) ya shige gaba don ya yi wa diyar Manzon Allah salla. Yana mai cewa: "Ya Ubangiji 'yar Manzonka ta yarda da ni, ya Ubangiji! hakika ta faku cikin kawaici, ka yaye mata. Ya Ubangiji an kaurace mata ka sadar da lta, Ya Ubangiji hakika an zalunce ta ka bi mata hakkinta, kai ne mafi alkhairin masu hukunci". Sannan sai ya yi mata salla raka'a biyu, ya daga hannuwansa sama yana cewa: "Wannan 'yar Manzonka ce Fatima, ka fitar da ita daga duhu zuwa haske".

An samu ruwayoyi daban-daban dangane da inda kabarin sayyida Zahara (a.s) yake, amma wasu sun tafi a kan cewa yana Bakiyya ne, wasu kuma sun tafi a kan yana cikin dakinta. lokacin aka fadada Masallacin Manzo (s.a.w) sai ya zama yana cikin Masallacin Manzo (s.a.w). Kodai mene ne ya faru an riga an boye kabarin nata kamar yadda ta yi wasiyya da hakan ga Imam Ali (a.s) domin ta nuna zaluntarta da wannan al'umma ta yi na rashin kula da hakkinta da na mijinta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next