Halayen Sayyida Zahara (s.a)



Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da halayen Sayyida Zahara (s.a) da rayuwarta.

Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da suke kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Sayyida Zahara (a.s) ta kasance babban misali abin koyi ga duk wanda yake son tsayawa kyam kan gaskiya da kare hakkinsa da kuma hakkin alأ¢â‚¬â„¢umma yayin da bayan wafatin babanta (s.a.w) ta tsaya ta dage wurin ganin ta kwaci hakkinta da gadonta, da kuma hakkin mijinta na jagorancin alأ¢â‚¬â„¢umma, da hakkokin alأ¢â‚¬â„¢umma na ganin sun samu mai shiryarwa zuwa ga tafarkin gaskiya da hasken shiriya da shariأ¢â‚¬â„¢ar Allah (s.w.t).

Ta kasance farkon wanda ya yi shahada kan kariya ga wilayar Imam Ali (a.s) da zuriyarta, da kuma wilayar manzon rahama (s.a.w), da kuma kana bin da ya shafi neman hakkinta wanda yake na dukiyarta ne da annabin rahama (s.a.w) ya ba ta shi kyauta tun lokacin yana da rai, sannan kuma da abin da ya shafi gadonta. Da wannan ne zamu ga ta kasance mutum na farko da ya fara nuna wa duniyar musulmi jajircewa a kan kwatar hakkinsu komai tsanani da wahala.

 Mafi tsananin lamari garta shi ne lamarin da ya shafi jagorancin alأ¢â‚¬â„¢umma bayan manzon Allah (s.a.w) alأ¢â‚¬â„¢amarin da ya sanya ta jaula da gewayawa gidajen ansar domin su ba ta gudummuwa amma ba ta samu wannan ba daga ko da mutum guda. Lamarin ya kai ta ga tattaunawa da halifan farko kan ya ba su hakkinsu amma abin ya ci tura, don haka ne ma aka samu jan daga mai wuyar gaske da musayan kalamai na magana kan wannan lamari tsakanin gidan Annabi (s.a.w) da kuma kuraishawa.

Sayyid Zahara (a.s) ta so ta nuna wa alأ¢â‚¬â„¢umma munin wannan lamarin na canja wasiyyar Annabi (s.a.w) da kawar da jagoranci daga cikin alayensa zuwa ga waninsu, da sakamakon da zai samu alأ¢â‚¬â„¢ummar musulmi na kauce wa koyarwar musulunci ta asali ta asasi. Amma alأ¢â‚¬â„¢umma ba ta amsa mata ba, saboda jahiltar sakamakon abin da ta tsoratar da su, da yawan mutane sun dauka cewa lamarin mulki ne kawai, sai dai abin ya fi karfin hakan kamar yadda ta yi nuni, don sai ga shi alأ¢â‚¬â„¢ummar musulmi ta kasu gida-gida sakamakon sabani kan mene ne gaskiyar hakikanin musulunci, kowa yana bin nasa son ran a matsayin shi ne gaskiya, aka jefar da alayen Annabi (s.a.w) a gefe babu wani mai biyayya ga tafarkinsu sai أ¢â‚¬ع©yan kalilan, wani abin mamaki da takaici ma sai aka bi su da bita-da-kulli da kisa, sannan mai bin tafarkin da suka shata ya zama abin kyama a cikin alأ¢â‚¬â„¢umma.

Fadima (a.s) ta kafa hujja kuma ta yanke duk wani hanzari ga wannan alأ¢â‚¬â„¢ummar yayin da ta nemi su bi ta suka ki, kuma ta nuna musu sakamakon da a yau alأ¢â‚¬â„¢ummar musulmi suke cikinsa na kasakanci, da rarraba, da son rai, da rashin kima da daraja. Ta yi fushi da alأ¢â‚¬â„¢umma amma duk da haka alأ¢â‚¬â„¢ummar ba ta fadaka ba, don haka ne ma ta yi wasiyya da kada wanda ya halarci janazarta sai Imam Ali (a.s) da أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanta da wasu kalilan da aka boye sunayensu don gudu kada a tilasta su nuna inda aka binne ta, don haka ne ma ya kasance abin kunya har yau ga duniyar musulmi domin ba su san kabarinta ba!.

Ta kasance mafi muhimmancin mutum da yake misalta mai hamayya da shugabancin Abubakar da duk wanda yake goyon bayansa, sannan kuma mutum mai kwarjini da kowa yake shayi, wasu masu tarihi sun kawo cewa Imam Ali (a.s) ya samu sauki a rayuwarta daga cutarwar masu jagoranci har sai bayan mutuwarta ne aka tilasta masa, aka takura rayuwarsa da kuntatawa mai tsanani!, har ma suna kawo cewa duk tilascin da aka yi masa bai yi baiأ¢â‚¬â„¢a ba sai bayan rasuwarta da ya kasance ba shi da wani mai ba shi kariyar siyasa!.

Ta kasance ita ce ta fi kowace mace kamewa a tarihin matan duniya, don haka ne ta tarbiyyantar da kanta da matan zamaninta cewa; abin da ya fi musu kyawu shi ne su lizimci gidansu sai dai gun lalura. Kamewarta ta kasance hatta da makaho tana sanya masa hijabi domin ita tana ganinsa idan shi ba ya ganinta!.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next