Halayen Sayyida Zahara (s.a)



 

Manzon Allah (s.a.w) ya tarbiyyantar da ita, ya yi mata nasihohi, ya kuma nuna mata hanyar da zata bi domin rabauta duniya da lahira. Sai ta bi dukkan shiriyarsa, sai ta kasance malama, mai sanin duk wata masأ¢â‚¬â„¢ala, kuma maأ¢â‚¬â„¢asumiya da ba ta taba yin sabo ba, kuma mai shiryayya mai shiryarwa ga alأ¢â‚¬â„¢umma, da alأ¢â‚¬â„¢umma ta bi ta bayan Manzon Allah (s.a.w) da ba a taba samun wani bata ko jahilci ba cikin duniya.

Ta sha wahala matuka a rayuwarta, ba don gudun tsawaitawa ba, da mun kawo da yawa daga cikin hikimomin Manzon rahama (s.a.w) da wasiyyoyin da ya yi mata na juriya kan wahalar da take sha, domin ba ta tarbiyya kan kowane janibi na rayuwa.

Sai dai yayin da zata bar duniya sakamakon abin da ya faru mai daci na zalunci a kanta, ta yi wasiyya ita ma ga Imam Ali (a.s) da ya boye janazarta da kabarinta, kuma ya yi aiki da dukkan wasiyyoyinta hatta wadanda suka shafi rayuwarsa bayan wafatinta. Ta yi masa wasiyya da matar da zai aura bayanta, da kuma raba kwana tsakanin matarsa da zai aura da أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanta Hasan da Husain (a.s) da sauran wasiyyoyi masu sanya kuka da hawaye Allah ya sanya mu cikin cetonta.

An yi wa Fadima (a.s) bazata a wata rana da mutuwar Abu Talib ammin Babanta[5] kuma shugaban Bani Hashim a lokacin ne ta san cewa lallai wani rukuni daga rukunan da Babanta (s.a.w) yakan dogara da su ya rushe saboda haka ta ji muryarsa tana rawa saboda bakin ciki, fukafukin da yakan tashi sama da su guda biyu an cisge dayan musamman saboda tsananin bakin ciki da ya mamaye zuciya da fuska madaukakiya.

Sai ta ga Babanta mai daraja (s.a.w) yana kuka a farkon ganin haka a rayuwarta da hawaye masu zafi da ke kwarara a kumatunsa masu albarka a lokacin duk wanda yake wannan duniya ya san cewa lallai akwai zafi da yake tafarfasa a cikin jini da tsuka na Annabin rahama don haka ne ma sai ta motsa da jiki mai haske da albarka ta sanya fararen hannayen nan da suke daga aljanna ne aka gina su, tana mai share masa hawaye masu zafi da fari da ke gudana suna diga kasa kamar أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan carbi dunkule-dunkule, wallahi na so a ce suna zuba ne a jikina domin in shafe su a fuskata domin kada ta samu shafa daga shedan har abada da takan kai ga toshe mahangar tunani, na kuma shafa a jikina domin kada ya sami kuna na wuta!.

Ta kasance tana mai shafewa da hannayenta masu daraja har ta kwantar da zogin da yake ji ta saukar da tafasar nan ta kunkunar juciyarsa ta kawar da abin da yake ji na rashi mai tsanani.

Amma ba a dade ba da أ¢â‚¬ع©yan kwanaki kadan sai ga musiba mafi girma ta sauka ta kasance, alhali ga wancan mikin bai warke ba aka sake tunbuke wa Manzon tsira daya fukafukin da ya rage, alhali da man ya yi rauni da yake zubar jini maras yankewa.

Wayyo Allah!! ba a dade ba sai na ji wata kalma da ta fito daga baki mai haske da kamshin da digonsa ya fi karfin almiskin da yake cikin duniya gaba daya, wace kalma ce? Kalma ce mai nauyi daga haske mai baki mai haske da ake cewa da ita Babar Babanta (a.s) tana cewa: Ina Babata!!.

Saboda haka jin wannan kalma ta sanya Manzo (s.a.w) ya ji wani suka da ya fi sukan kibiya ciwo domin uwa ce ta hakika take tambayar mata ta hakika da suke da wadancan alakoki biyu da mafi girman halitta (a.s) uwa ce kuma أ¢â‚¬ع©ya amma ba tare da an sami abin da masu ilimin falsafa da suke cewa gewayo ba, wato na farko ya koma na karshe, ga hawaye yana zuba kamar ana mamakon ruwa mai kwarara, kai alأ¢â‚¬â„¢umma ku ji wannan kalma mai nauyi da ke kunshe cikin tambayar uwa ga dan da yake uba gareta da take cewa ina Babata?!!.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next