Halayen Sayyida Zahara (s.a)



Haka nan Fadima ta sha wahala tana mai cire kayoyi daga digadigan Babanta tana mai shafe masa jini daga kafafunsa tana mai wanke hannyansa da shafe masa kasa daga fuskarsa tana mai kawar da bakin cikin nan na أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan hanji da kayan ciki daga bayansa da kirjinsa, har shekarar ta ta tara ta wuce.

Babanta ya kasance karkashin zaluncin masu makwabtaka da shi har ta wayi gari tana mai nemansa wata rana sai ta yi kicibis da kazanta a kansa da kasa da kayoyi, saboda haka ta gaggauta tana mai kawar da wannan da hannayenta masu niأ¢â‚¬â„¢ima tana mai kuka saboda abin da ya sami Babanta na daga cutarwar Kuraishawa da gabarsu da kuma cutarwar makota da makusantansa daga Bani Abdi Manafi, sai wannan ya sanyaya masa zuciya, fushinsa ya kau, zuciyarsa ta kwanta hankalin أ¢â‚¬ع©yarsa ya faranta, tana mai kuka daga halin da ta gan shi a ciki, shi kuma yana mai ce mata: أ¢â‚¬إ“Kada ki yi kuka ya أ¢â‚¬ع©yata Allah zai kare Babankiأ¢â‚¬â€Œ.

Kafirai ba su kyale Fadima (a.s) ba kamar yadda ba su kyale Babanta ba kamar yadda wani mafi wautarsu Abu Jahal (L) ta ji shi yana zagin Babanta (s.a.w) saboda haka ne ma ta kasa mallakar kanta ta yi raddi ga shi Abu Jahal (L) da kalmomi masu hikima da ke cike da fasahar nan ta Bani Hashim amma saboda Abu Jahal ba shi da kunya da mutunci bai san shi ba har abada, sai ya daga hannunsa ya mare ta a fuskarta yana mai ci gaba da zagi da cin mutunci ga Manzo (s.a.w), Fadima (a.s) ta tafi tana mai bakin ciki da kuka sakamakon abin da yake yi wa Babanta, har ta wuce wuri da Abu Sufyan yana mai jin kukanta da ganin hawaye na zuba a kumatunta (a.s) yana mai tambayar ta me ya same ki ya أ¢â‚¬ع©yar Muhammad!

Haka nan wata rana Fadima (a.s) ta wuce wasu mutane daga manyan Kuraishawa suna shawara kan alأ¢â‚¬â„¢amarin Muhammad (s.a.w) sai ta ji wasu suna cewa: Wallahi ba ma ganin Muhammad (s.a.w) zai daina abin da yake yi, idan mu ka kyale to lallai zai shuna mana bayinmu a kanmu da maأ¢â‚¬â„¢aikatanmu, kuma zai canza matanmu da أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanmu ta yadda babu wata dubara da zata rage garemu, me kuke gani?.

Abu Jahal (L) ya motsa yana mai cewa ina ganin ku kashe shi kawai. Sai wani ya ce: Yaya zamu yi da fushin Bani Hashim da takubban dakarunsu?. Abu Jahal ya ce: Amma yadda za a yi shi ne, kowanne daga cikinku ya dake shi da takobi dukan kwaf daya sai ku yi musharaka a jininsa gaba daya ta yadda Bani Hashim ba za su iya daukar fansa ba sai dai maganar diyya.

Da Fadima ta ji wannan magana sai zuciyarta ta cika da tsoro a kan Babanta, ta lizimci wajan, ta ki barinsa, idanunta suna kula da hanya har sai ta ga Babanta ya bullo da sauri sai ta gaya masa duk abin da Kuraish suka yi  na makirci da kaidi.

Sai ya gaya mata cewa kada ta damu: أ¢â‚¬إ“Ki tabbata ya أ¢â‚¬ع©yata Allah ba zai taba ba su dama a kan Babanki baأ¢â‚¬â€Œ. Annabi ya wuce masallaci har sai da ya shiga ya wuce mutanen da suke mitin a kansa domin kashe shi, sai suka yi shiru suka rufe idanunsu saboda abin da suka gani a fuskarsa na haiba da kwarjini, suka mance abin da suka yi ittifaki a kansa dazu, har sai da Manzo (s.a.w) ya tsaya a kansu ya dauki kasa jimki daya ya watsa a kansu yana mai cewa: أ¢â‚¬إ“Fusaku sun muzantaأ¢â‚¬â€Œ.

Sannan ya fuskanci Kaأ¢â‚¬â„¢aba ya yi salla ga Allah madaukaki (s.w.t) a kusa da su, Fadima (a.s) tana tsaye tana ganinsu ba wanda ya motsa daga cikinsu kamar ba wanda ya gan shi, yayin da ya gama sallarsa da munajatinsa sai ya rike hannun أ¢â‚¬ع©yarsa suka tafi gida tare!

Haka nan ta sami wani kunci mai yawa na abin da ta gani wata rana, Babanta yana salla a Kaأ¢â‚¬â„¢aba, ga Abu Jahal (L) da wasu daga Kuraishawa kamar su Asi dan Waأ¢â‚¬â„¢il Assahami da Haris dan Kais Assahami (L) suna yanka rakumi. Sai Abu Jahal da Umayya dan Khalf (L) suka waiga suka ce da yaransu: Waye zai zo mana da mahaifar rakumin Bani Saham sai ya dora shi a kan bayan Muhammad! (s.a.w) idan ya yi sujada?

Wannan tunani ya yi wa wasunsu daidai Ukuba dan Abi Muأ¢â‚¬â„¢id (L) da Utba da Shaiba أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan Rabiأ¢â‚¬â„¢a (L) suka tashi suka dauko tunbi da mahaifar suka dora kan kafadun Manzon Allah (s.a.w) yana mai sujada.!



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next