Halayen Sayyida Zahara (s.a)



Hudubarta mai fasaha da balaga da hikimomi da babu kamarsu ta shahara matuka, alhalin a lokacin ba ta wuce shekaru goma sha takwas ba, amma ta zo da hikimomin da suka dimautar da masu hankula da masu sauraro har a nade duniya, da wannan ne ta cancanci kasancewa kwafi ce ta babanta (a.s).

Kuma ba mamaki gareta domin ita أ¢â‚¬ع©yar babanta ce, kuma matar mijinta, wadanda duniya ba ta haifi kamarsu ba a cikin fasaha da magana ba. Don haka ne maganarta ta kasance mashaya ce da ta bubbugo daga wadannan manyan koguna guda biyu marasa gaba da iyaka, sai ta fesa wannan hasken na hikima da ya mamaye sasannin dukkan أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanta tsarkaka tun daga kan Imam Hassan (a.s) har zuwa kan Imam Mahadi (a.s).

Sannan zamu ga abin da ta zo wa duniya da shi na rahama wanda har yanzu kowa yana cin albarkacinsa, yayin da ta nemi a ba ta أ¢â‚¬ع©yar hidima daga cikin bayin da aka kawo da zata taimaka mata a aiki, sai aka ba ta zabi ko tasbihi ko أ¢â‚¬ع©yan aiki, sai ta zabi tasbihi wanda dukkan alأ¢â‚¬â„¢umma zasu amfana da shi har alkiyama ta tashi. Don haka ne bayan salla aka so kowane mai salla ya yi wannan tasbihi, da fara da kabbara 34, da hamdala 33, da tasbihi 33, ga Allah madaukaki wanna kuwa ana kiran sa da tasbihin Zahara (a.s).

Ta ruwaito hadisai masu yawan gaske a kowane janibi da ya hada da; siyasa, tattalin arziki, zaman tare, rayuwar al'umma, hakkoki, hukunce-hukunce, ibadoji, da mu'amaloli, da sauransu. Wannan lamari ne da yake bukatar tsawaitawa don haka ba zamu fada cikinsa ba.

Sayyida Zahara (a.s) ita ce macen da take cikakkiya ta kowane janibi da dukkan mata ya kamata su dukufa wurin neman saninta, da koyi da ita a dukkan janibobin rayuwarta ta zaman alأ¢â‚¬â„¢umma, da ta cikin gida, da ta waje, da ta muأ¢â‚¬â„¢amala da mutane, da jagoranci da makamantansu.

Matan da suke son zama kammalallun mata masu daraja a duniya to sai su yi koyi da mata masu daukaka kuma su dauki samfurin rayuwar zaman tare daga Imam Ali (a.s) da sayyida Zahara (a.s), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (a.s) ya shiga wajan Fadima (a.s) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu. Sai ta ce: أ¢â‚¬إ“Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komaiأ¢â‚¬â€Œ. Sai ya ce: أ¢â‚¬إ“Me ya sa ba ki gaya min baأ¢â‚¬â€Œ Sai ta ce: أ¢â‚¬إ“Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shiأ¢â‚¬â€Œ[1].

Daga Saifu, daga Najmu, daga Abu Jaأ¢â‚¬â„¢afar (a.s) ya ce: أ¢â‚¬إ“Hakika Fadima (a.s) ta lamunce wa Imam Ali (a.s) aikin gida da kwaba gari da yin gurasa da share gida, shi kuwa ya lamunce mata abin da yake bayan kofa: yin itace, kawo abinciأ¢â‚¬آ¦ sai wata rana ya ce da ita: Ya Fadima shin kina da wani abu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama hakkinka ba mu da komai tun tsawon kwana uku ke nan sai dai abin da muka tanadar maka kai kadai, sai ya ce: Me yasa ba ki ba ni labari ba? Sai ta ce: Manzon Allah (s.a.w) ya hana ni in tambaye ka wani abu, ya ce da ni: Kada ki tambayi dan amminki wani abu, in ya zo da shi, shi ke nan, in ba haka ba to kada ki tambaye shiأ¢â‚¬â€Œ.

Yahaya da sanadinsa daga Abi Sa'idul khuduri, ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari sai ya ce da Fadima (a.s): Ya Fadima shin kina da wani abu da zamu ci. Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta babu wani abu da ya kwana gunmu da zamu ciyar da kai shi yau, ba ni da komai kwana biyu ke nan sai abin da na zabe ka a kaina da shi da kuma abin da zabi wadannan biyu أ¢â‚¬â€œtana nufi Hasan da Husain- a kaina da shi. Sai ya ce: Don me ba ki gaya mini ba sai in samo miki wani abu? Sai ta ce: Ni ina jin kunyar Allah in kallafa maka abin da ba zaka iya ba, kuma ka kasa samu[2].

Daga Abil mufaddal, ya ce[3]: Muhammad dan Jaأ¢â‚¬â„¢afar dan Kais dan Maskana ...da dogon sanadinsa sai a koma wa littafinأ¢â‚¬آ¦ daga Abi Sa'idul khuduri ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari mai yunwa, sai ya ce: Ya Fadima, shin kina da wani abu da zaki ciyar da mu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta, ya girmama ka da wasiyya, babu wani abu da ya wayi gari a wajenmu da zamu ciyar da wani mutum shi tun kwana biyu ke nan sai abin da na fifita ka da kai da Hasan da Husain da shi a kaina. Ya ce: Har da ma yara biyu! Me yasa ba ki sanar da ni ba sai in zo muku da shi? Sai ta ce: Ya Abal Hasan, ina jin kunya daga ubangijina in kallafa maka abin da ba zaka iya baأ¢â‚¬â€Œ[4].

Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (a.s) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next