Halayen Sayyida Zahara (s.a)



Fadima (a.s) ta ga abin da aka yi wa Babanta sai ta gaggauta tana mai jin zogi da bakin ciki mai tsanani a kan abin da ta ga ni, hawayenta suna kwarara a kan kumatunta, saboda haka sai ta bayar da duk kokarinta wajan ganin ta kawar da wannan dauda daga kafadun Babanta (s.a.w), Annabi mai girma Uba mai rahama ya daga kansa yana kallon أ¢â‚¬ع©yarsa Fadima (a.s) idanunsa cike da rahama da tausayi da kauna da yarda da bege gareta, tare da dukkan abin da zuciya zata iya nuna wa na nutsuwa da tabbata da hakuri, sannan sai ya rike hannayenta tsarkaka ya tattaro ta zuwa kirjinsa madaukaki ya ce: أ¢â‚¬إ“Mamakin yadda kika zama babar babanki da wuri haka Ya Fadimaأ¢â‚¬â€Œ[8].

Bai bar wannnan waje mai daraja ba tare da ita, wajan da kafiran Kuraish suka bata da dauda sai da ya daga hannayensa zuwa sama yana mai adduأ¢â‚¬â„¢a yana cewa: Ya Allah! ina kai karar Abu Jahal (L) da Utba da Shaiba أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan Rabiأ¢â‚¬â„¢a (L)  a wurinka ka. Ya Allah! ina kawo karar Umayya dan Khalf (L) da Walid dan Utba (L) da Ukuba dan Abi Muأ¢â‚¬â„¢id (L) daأ¢â‚¬آ¦[9].

Kada ka so ka ga irin farin cikin Fadima أ¢â‚¬ع©yar Manzo (a.s) a wannan rana sakamakon irin matsayi da ya ba ta na wannan kalma ta (Babar Babanki) da ya daukaka ta zuwa gare shi, kamar yadda ta iya sanya wa a ran Babanta (s.a.w) a wannan ranar da aka samu haduwa a ruhi guda biyu da haduwar kanshi da kanshi, kuma haske da haske, cewa ruhin Baban (s.a.w) mai kira zuwa ga Allah ya samu sanarwa daga ruhin أ¢â‚¬ع©yar mai neman ta zama uwa ga Baban (a.s) cewa ruhinta ruhi ne mai cike kuma kunshe da tausayi irin na uwa ga uban kuma kariya mai karfi mahalarciya a kowane abu da ya faru ga uban (s.a.w), wanda sau da yawa irin wadannan abubuwa suka yawaita bayan Kuraishawa sun samu dama da wafatin Abu Talib!!, sanarwar da ruhin uban ya samu daga ruhin أ¢â‚¬ع©yar shi ne cewa ita uwa ce, don haka ta cancanci wannan kalam ta Babar Babanta.

Fadima (a.s) ita Kadai Ce أ¢â‚¬ع©Yar Annabi (s.a.w) saboda wasu dalilai masu karfi da suka hada da: Na farko: Ambaton أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢ya da jamأ¢â‚¬â„¢i a fadinsa madaukaki cewa: أ¢â‚¬إ“Ya kai Annabi ka gaya wa matanka da أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanka da matan muminai su sassauto da mayafansu wannan shi ya fi da a san su domin kada a cutar da su, kuma hakika Allah ya kasance mai gafara mai rahama.

Wannan alأ¢â‚¬â„¢amari ba ya nuna cewa manzon Allah (s.a.w) yana da أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢ya sama da daya, alأ¢â‚¬â„¢amarin yana kan kaddarawa ne da ba dole ya kasance yana da samuwa ta zahiri ba, kuma akwai da yawa a kurأ¢â‚¬â„¢ani inda aka yi maganar jamأ¢â‚¬â„¢I na gaba daya amma ana nufin abu daya da shi kamar yadda Allah yake fada a cikin ayar mubahala da cewa: أ¢â‚¬إ“idan suka yi jayayya da kai kan alأ¢â‚¬â„¢amarinsa to ka ce ku zo mu kira أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanmu da أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanku da matanmu da matanku da kawukanmu da kawukanku sannan sai mu yi adduأ¢â‚¬â„¢a mu sanya laأ¢â‚¬â„¢ana kan makaryataأ¢â‚¬â€Œ (aali imrana: 61).

Kuma dukkan musulmi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da kawukanmu shi ne Annabi (s.a.w) da kuma Imam Ali (a.s), mata kuma wanda jamأ¢â‚¬â„¢I ne ana nufin Fadima Zahara (a.s) أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢ya kuma wanda shi ma jamأ¢â‚¬â„¢I ne ana nufin Imam Hasan da Husain (a.s).

Na biyu: Malaman Shi'a suna da wani raأ¢â‚¬â„¢ayi kan wannan alأ¢â‚¬â„¢amari, akwai masu ganin Rukayya da Zainabi da Ummu kulsum أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan Annabi (s.a)  ne, wasu kuma suna ganin agololinsa ne kuma أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan Hala أ¢â‚¬ع©yarأ¢â‚¬â„¢uwar sayyida Hadiza (a.s) da babarsu ta mutu sai sayyida Hadiza (a.s) ta dauki rainonsu, suna ganin cewa Hadiza ta kasance budurwa ba ta yi wani aure ba kafin Annabi (s.a), kamar yadda aka yada game da ita ba, kuma wannan shi ne ya fi kusa da gaskiya, kuma ita ce magana mai karfi.

 

Ibn Shahri Ashub ya fada cewa: أ¢â‚¬إ“Ahmad Bilaziri ya ruwaito, haka ma Abul kasir alkufi a littattafansu, da murtadha a cikin Shafi, da Abu Jaأ¢â‚¬â„¢afar a cikin talkhis cewa Annabi (s.a.w) ya aure ta tana budurwa ne, kuma wannan yana karfafa abin da aka fada a littattafan Alanwar da albidaأ¢â‚¬â„¢I cewa Rukayya da zainab أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan Hala أ¢â‚¬ع©yarأ¢â‚¬â„¢uwar Hadiza neأ¢â‚¬â€Œ[10].

Kuma su maأ¢â‚¬â„¢abota wannan raأ¢â‚¬â„¢ayi suna da dalilansu a cikin littattafan hadisai da na nasabobi da na tarihi[11].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next