Mukamin Ahlul-bait



 

Wannan lambar girma da daukaka tana da manufa da abin da take nuni da shi a kebance, wanda ya kamata musulmi su kiyaye shi kuma su riski zurfinsa.

Ta Uku: Ayar Mubahala

فَمَنْ حاجَّكَ فيهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءكَ ك مِنَ الْعِلْمِ فَقُل تَعالَوا نَدْعُ أبْنَاءَنَا وأبْنَاءَكُمْ ونِسَاءَنَا ونِسَاءَكُمْ وأَنْفُسَنَا أنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَةُ الله عَلى الكَذِبين

"To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'an nan kuma mu kankantar da kai, sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". (Surar Ali Imrana, 3: 61)

Wani abu mai madauwamin tarihi wanda malaman tarihi da tafsiri sun ruwaito shi ya auku, wanda kuma yake nunawa al'umma irin girma da daukakan Ahlulbaitin Manzon Allah (S.A.W), su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S) a wajen Allah (S.W.T.) da kuma matsayinsu a cikin wannan al'umma.

Wannan abin kuwa kamar yadda su malaman tafsiri da tarihin suka kawo shi ne cewa wata tawaga([14]) ta kiristocin Najran ta zo domin ta yi jayayya da Manzon Allah (S.A.W) don a gane waye yake kan gaskiya. Nan take sai Allah Ya umurce shi cikin wannan aya mai albarka da ya kira Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S) ya fita da su zuwa wani kwazazzabo, ya kuma kira Kiristocin da 'ya'yansu da matansu su fito sannan a yi addu'ar Allah Ya saukar da azaba kan makaryata.

Zamakhshari a cikin Al-Kashshaf yana cew a: "Yayin da Manzon Allah (S.A.W) ya kiraye su zuwa ga Mubahala([15]), sai suka ce: sai mun koma mun yi nazari. Da suka kebanta sai suka ce wa shugabansu; "Ya Abdul Masih! Me ka ke gani? Sai ya ce: "Wallahi, Ya ku jama'ar Nasara, kun sani cewa Muhammadu Annabi ne wanda aka aiko shi kuma hakika ya zo muku da bayani mai rarrabewa game da al'amarin sahibinku. Wallahi babu wata al'umma da ta taba yin mubahala da wani Annabi face babbansu ya halaka, karaminsu kuma ya gagara girma, to idan ko kun aikata hakan to lallai za mu halaka. Idan kun zabi riko da adddininku da zama bisa abin da kuke kansa to ku yi bankwana da mutumin na Larabawa, ku koma garinku.

Ko da gari ya waye sai Manzon Allah (S.A.W) ya fito yana mai sammako, yana

rungume da Husaini (A.S) yana rike da hannun Imam Hasan (A.S), Fadima (A.S) kuwa tana biye da shi sannan shi kuma Aliyu (A.S) yana bayanta, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce musu: "Idan na yi addu'a ku ce amin".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next