Mukamin Ahlul-bait




[1] Tirmidhi juzu'i na 2 cikin "Manakib Ahlulbaiti" shafi na 308 daga Umar ibn Abi Salama, wanda ya ce: an saukar da ayar "…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" a gidan Ummu Salma. Daga nan sai Manzon Allah (S.A.W) ya kira Fadima, Hasan, Husaini da Ali ya rufe su da mayafi, ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaiti, don haka Ka tafiyar da kazamta daga gare su Ka tsarkake su tsarkakewa". Sai Ummu Salma ta ce: "Ya Manzon Allah shin ni ma ina daga cikinsu ne?, sai ya ce mata: "Ke dai kina a matsayinki, ke kina a kan alheri".

[2] An ruwaito wannan hadisi cikin littafin Ghayat al-Maram daga Abdullah ibn Ahmad ibn Hambal ta hanyoyi uku daga Ummu Salama, haka nan ma cikin Tafsirin Tha'alabi…haka nan ma Ibn Mardawihi da Khadib daga Abi Sa'id Khudri da wannan ma'ana sai dai kawai 'yan canje-canje na lafazi. Haka nan kuma an ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram daga Abdullahi bn Ahmad bn Hambal daga babansa da isinadinsa zuwa ga Ummu Salama, dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i kan Ayar Tsarkakewa. Wanda kuma ya ke son karin bayani kan wasu masdarori na musamman kan tafsirin wannan aya da kuma gabatarwa kan Ahlulbaiti guda biyar (A.S) to sai ya karin bayani da ke karshen wannan littafi.

[3] Ibn Jarir da Ibn Abi Hatam da Dabarani sun ruwaito wannan hadisi daga Abi Sa'id Khudri, kamar yadda kuma aka ruwaito shi cikin Ghayat al-Maram da Tha'alabi cikin tafsirinsa, a cikinsa Tirmidhi ya ruwaito shi kuma ya ingantar da shi, da kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Hakim, kuma duk sun ingantar da shi. Haka nan ma Ibn Mardawihi da Baihaki cikin Sunan dinsa ta hanyar Ummu Salma. Dubi Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an na Allama Tabataba'i.

"…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([3])".

[4] Ibn Mardawihi daga ibn Abi Shaibah da Ahmad da kuma Tirmidhi sun ruwaito kuma sun inganta shi, sannan kuma Ibn Jarir da Ibn Munzir da Dabarani da Hakim, kuma sun inganta shi, da kuma ibn Mardawihi daga Anas. Mai son karin bayani sai ya duba Al- Mizan na Tabataba'i yayin da yake magana a kan Ayar Tsarkakewa.

[5] Jami al Usul, juzu'i na 9, shafi na 156 ya nakalto daga Sahih Tirmidhi, haka nan ma Hakim ya ruwaito shi cikin Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 158, kuma ya inganta shi.

[6] Fadhl Aalulbaiti na Takiyuddin Ahmad bn Aliyu al Makrizi (wanda ya rasu a shekara ta 845 bayan hijira), shafi na 21.

[7] Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.

[8] Ghayat Maram yayin tafsirin ayar.

[9] Sanannen al'amari ga mai karatu cewa wannan fassara ta yi nisa ga hakikanin ma'anar kalmar, don kuwa ma'anar kalmar aal a cikin harshen Larabci a fili yake, babu yadda za a fassara kalmar aal da al'umma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next