Mukamin Ahlul-bait



Fakhrurrazi ya kawo cikin tafsirinsa Alkabir kwaton-kwacin abin da Zamakhshari ya ruwaito, inda tafsirinsu suka dace da juna a wannan matsayin. Sannan ya yi karin bayani a kan zancen Zamakhshari da cewa:

"Ka sani cewa wannan ruwaya daidai take da abin da aka daidaita a kan ingancinsa tsakanin ma'abuta tafsiri da hadisi([18])".

Allama Tabataba'i ya ce wadanda ake nufi a wannan aya kuma wadanda Allah Ya yi nufin (amfani da su wajen) tsinewa abokan gabarsu, su ne Manzon Allah

(S.A.W), Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S). Ga abin da Allama Tabataba'in ya ce: "Malaman hadisi sun hadu a kan ruwaito wannan ruwaya da samun karbuwarta, kuma ma'abuta manyan littattafai kamar su Muslim a cikin Sahihinsa da Tirmidhi a nasa Sahihin, sun tabbatar da wannan ruwaya, sannan malaman tarihi sun karfafa ta.

Kana kuma malaman tafsiri sun hadu a kan kawo wannan ruwaya cikin tafsiransu ba tare da wata suka ba, ba kuma kokwanto. Haka nan kuma akwai malaman hadisi da tarihi kamar su Dabari da Abul Fida da Ibn Kathir da Suyudi da sauransu".  A cikin wannan aya mai albarka, Allah da ManzonSa  Sun yi amfani da Ahlulbaiti (a.s) wajen yin Mubahala da abokan gaban Allah, to hakan kuwa yana sanar da al'umma matsayi da daukakan da suke da shi. Hakika ba don wannan kebantacciyar daukaka da suke da ita a wajen Allah ba, da kuma tsarki na musamman ma ba, da Manzon Allah (S.A.W) bai kira wadannan taurari tsarkaka domin yin barazana ga makiya Allah da saukar da azaba da kuma lamunce amsa addu'arsu ba.

A cikin ayar akwai ma'anoni masu zurfi na harshen da aka yi amfani da shi cikin maganar wadanda lallai ne a yi la'akari da su, hakan kuwa shi ne danganta wadannan Taurari (Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini) da Annabi (S.A.W), wato cewan da aka yi "'ya'yanmu" da "matanmu" da "kanmu".

Ba don faruwar wannan lamari da fitar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi da wadannan Taurari tare da shi ba, da mai yiyuwa zukata su koma ga matan Annabi (S.A.W) wajen kalmar "matanmu", wajen kalmar "'ya'yanmu" kuwa zuwa ga Fadima da sauran 'ya'yan Ma'aiki (S.A.W), sannan wajen kalmar "kanmu" kuwa zuwa ga zatin Annabi (S.A.W) mai tsarki shi kadai.

Amma fita da wadannan mutanen hudu da Annabi ya yi tare da shi koma bayan wasunsu, ya fassara mana cewa mafificiyar macen wannan al'umma kuma abin koyi gare ta ita ce Nana Fadima (A.S), zababbun 'ya'yan musulmi kuwa su ne Hasan da Husaini (A.S), don kuwa Alkur'ani ya dangantasu ga Annabi (S.A.W) sai suka zama 'ya'yansa, kamar yadda aya ta nuna. Kana kuma Alkur'ani ya dauki Aliyu (A.S) tamkar ran Manzo (S.A.W).

Ta Hudu: Ayar Salati

() إنَّ الله ومَلائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلى النَّبِيّ يأيُّهَا الَّذينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وسَلِّموا تَسليمًا()



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next