Mukamin Ahlul-bait



 "...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)

 Da kuma fadinSa cewa: "...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina....". (Surar Nur, 24: 63)

 "Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah...." (Surar Ahzabi, 33: 21)

 Addu'a ga dangin Manzo tana da wani matsayi mai girma, domin haka ne aka sanya wannan addu'ar ta zama cikamakin tahiya a cikin salla, wato: "Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kuma Ka yi jin kai ga Muhammadu da Alayen Muhammadu"([10]). Ba a samun wannan girmamawa ga wani wanda ba su dangin ba. To duk wannan yana nuni da cewa kaunar alayen Muhammadu wajiba ce. Imam Shafi'i yana cewa:

Ya kai mahayi tsaya a wannan kwari na Mina,

Ka kira mazaunin al-Nahidhi.

Da daddare yayin da alhazai suka wuce zuwa Mina,

Tamkar kogin Furatu mai yalwa da yawan ruwa.

Idan Rafdhu(1) shi ne son Zuriyar Muhammadu,

To mutane da aljannu su shaida ni Rafidhi ne([11]).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next