Mukamin Ahlul-bait



Dogewar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi, wata da watanni bisa tsayuwa a bakin kofar Aliyu da Fadima (A.S) yana kiransu da asuba zuwa salla, yana kiransu da Ahlulbaiti ba kome ba ne face sanar da al'umma mutanen da ake nufi da Ahlulbaiti, kana kuma yana fassara wa musulmi ayar tsarkakewa, yana sanar da su matsayin Ahlulbaiti (a.s) tare da jan hankulansu zuwa gare su da kuma wajabta musu kaunarsu da yi musu biyayya da jibinta al'amari gare su. Dabarani ya ruwaito daga Abu Hamra' cewa:

"Na ga Manzon Allah (S.A.W) yana zuwa kofar Aliyu da Fadima tsawon wata shida yana cewa: "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa[5]

Fakhru al-Razi ya ambata a cikin tafsirinsa, Tafsir al Kabir, cewa bayan saukar ayar: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta", (Surar Daha, 20: 132), Manzon Allah (S.A.W) ya kan je (kofar) Aliyu da Fadima kowace safiya yana mai cewa: (lokacin) salla (ya yi), ya aikata hakan har na tsawon watanni.

Sannan kuma ya kawo hadisin Hammad bn Salma, daga Aliyu bn Zaid daga Anas cewa: "Annabi (S.A.W) ya kasance yana wucewa ta dakin Fadima koyaushe ya fito zuwa ga salla har na tsawon wata shida, yana mai cewa: "Salla! Ahlulbaiti! "Allah Na

nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([6])".

A cikin wannan akwai bayani da kuma nuni zuwa ga muhimmancin da Manzon Allah (S.A.W) ya riki Ahlulbaiti (a.s) da shi, da kuma karfafawarsa wa musulmi cewa su (Aliyu, Fadima da 'ya'yansu) su ne mutanen gidansa (Ahlulbaiti), wadanda Allah Ya tafiyar da dukkan dauda ga barinsu, Ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Wannan muhimmancin an nuna shi ne bayan Allah Ya yi magana da ManzonSa cewa: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta".

Sannan a sarari yake cewa daga abin da ayar: "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa", take nuni da shi da kuma amfani da lafazin maza ba lafazin mata ba da aka yi, wato (عنكم) da kuma (يطهِّركم), akwai nuni zuwa ga wadanda ake nufi, su ne wadannan mutane biyar din. Bayani ya zo a cikin Tafsirai cewa da Allah Yana nufin matan Annabi (s.a.w.) ne da Yayi amfani da kalmar (عنكنّ) da ta (يطهِّركنّ) da magana irin wacce ake yi wa mata.

A baya mun riga da mun ga Hadisin Mayafi lokacin da aka saukar da wannan aya ta tsarkakewa yayin da Ummu Salama taso shiga cikin wannan mayafi amma Manzon Allah (S.A.W) ya ce mata ke dai kina a matsayinka, kuma kina a kan alheri.

Hakan yana nuna mana rashin shigar matayen Annabi (S.A.W) cikin wannan aya ta tsarkakewa, kana kuma babu daya daga cikinsu da ta yi ikirarin saukar wannan aya a kansu, duk kuwa da cewa ayar ta falaloli da kuma matsayi mai girma ce. Wannan ayar ta fitar da wata hanya wacce abin da take nuni da shi da abin da ta tattara suna da yalwar gaske. Tana jan hankulanmu zuwa ga batutuwa na asasi a rayuwar Musulunci domin kada mu sami rikitarwar fahimta balle ma manufofin Littafin Allah na gaskiya su tawaya. Allah Ya yi nufin gina al'umma bisa ginshikin tsarki da nisantar dauda da abin kunya sai Ya sanya Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani tushe abin dogara da kuma haske mai haskakawa. Lalle babu wani mutum da Alkur'ani mai girma ya siffanta shi da wannan siffa daga cikin musulmi, babu kuma wanda Manzon Allah (S.A.W) ya siffanta shi da wannan siffar (siffar tsarki maras iyaka) face Ahlulbaiti (a.s).

Ta Biyu: Ayar Soyayya



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next