Mukamin Ahlul-bait



"Lalle, Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56)

A cikin ayoyin da suka gabata, Alkur'ani mai girma ya yi magana a kan tsarkin

Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu da kuma cewa su ne mutanen gidan Manzon Allah (S.A.W). Masu fassara kuma sun iyakance wadannan mutane da sunayensu cewa su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S).

To wannan ayar kuwa ta kawo umurni ne na wajibcin yin salati ga Annabi (S.A.W) da alayensa madaukaka da kuma kebancesu, koma bayan wasunsu da kuma girmama mukaminsu da karamarsu domin al'umma ta san matsayinsu wajen sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma.

Fakhrurrazi ya kawo cikin Tafsirinsa abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W) kan tafsirin wannan aya mai albarka, inda ya ce: "An tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "Ku ce: Ya Allah Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi tsira ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, Ka yi albarka ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai Abin godiya ne, Mai girma".

Kafin ya kawo wannan nassin, sai da ya bijiro da tafsirin ayar sannan ya ce:

"Wannan dalili ne kan mazhabar Shafi'i domin umurnin na wajibci ne([19]) saboda haka salati ga Annabi yana wajabta. Kuma salatin ba ya wajaba in ba a tahiya ba, saboda haka yana wajaba ne a cikin tahiya([20])".

Fakhrurrazi ya karkare da cewa: "Idan Allah da Mala'ikunSa sun yi wa Manzon

Allah (S.A.W) salati, to wata bukata kuma yake da shi ga salatinmu?

To muna iya cewa yi masa salati ba wai don yana bukatuwa ga salatin ba ne, don kuwa idan ba haka ba ne, to ai babu bukatar salatin Mala'iku bayan salatin Allah a gare shi. Amma ba kome ba ne yasa muke masa salati face bayyana girmamawarmu gare shi, da tausayawarSa gare mu domin Ya saka mana domin salatin. Don haka ne Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Wanda ya yi mini salati sau guda, Allah Zai masa goma").



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next