TSari Da Kayyade Iyali



Al’amari na biyu: Haihuwa da hayayyafa an karfafe su a musulunci kuma Kur’ani da Sunna sun kwadaitar da haka kamar fadinsa Madaukaki cewa: “Dukiya da ‘ya’ya kawar rayuwar duniya ce”[5]. Haka nan hadisai sun zo suna masu kwadaitarwa a kan haka: Kamar hadisin Bakar dan Salih ya ce: Na rubuta zuwa ga Abul Hasan (A.S) cewa: Ni na nisanci haihuwa shekaru biyar kenan domin matata ba ta son haihuwa, tana cewa: Yana yi mata wahala ta tarbiyyatar da su saboda karancin abin hannu. Sai (A.S) ya rubuta masa da cewa: Ka nemi haihuwa domin hakika Allah zai arzuta su[6]. Da sauran gomomin ruwayoyi da suke karfafa neman haihuwa da yawaitar al’ummar Manzo (S.A.W)

Amma matsalar a yau ba ta neman da na gari ko haihuwa da samurwar al’ummar duniya ta tsayu a kanta ba ne, maganar ita ce, Idan mutane sun yawaita da ya zama ana ji wa al’umma tsoron faruwar wani bala’i a cikin al’umma shin ya halatta a kayyade iyali ko tsara su.

Gabatarwa Kan Hukuncin Kayyade Iyali

Ba makawa cewa musulunci ya yarda da Tsara Iyali ko kayyade su idan an sami matsalolin da muka ambata a farkon wannan bahasi ko ba sa samu ba, Sa’annan Kur’ani mai girma ya kayyade lokacin shayarwa da shekaru biyu, an kuma hana shayar da yaro nonon mai ciki domin yana cutar da mai shan nonon, abin da wannan al’amari yake nunawa kuwa shi ne; tsayar da samuwar ciki har lokacin shayarwa ya wuce. Kamar yadda babu sabani a kan cewa ya halatta a tsayar da haihuwa sabaoda karancin lafiya da rauni da kan iya samun mace ko kare abin haihuwa daga rashin lafiya da yakan dauka daga Uwa kamar Uwa mai cutar tsida.

Wannan duk yana nuna cewa shari’a mai tsarki tana neman tsari ga iyali da karfafawa ga rayuwa ta gari mai inganci da yalwar rayuwa, da kuma aiki da tsarin da zai kai ga lafiyar al’umma da kiyaye yaduwarta bisa tsari na lafiya da aminci domin kada bala’i ya yadu a cikin al’umma ko lalaci a cikin tsarinta. Wannan kuma yana iya kasancewa ne idan an sami daya daga iyaye yana da muguwar cuta da ‘ya’ya sukan iya dauka, ko dakatar da samun cikin domin uwa ta samu damar shayar da danta da take shayarwa, ko tsoron kada ta kasa tarbiyyatar da ‘ya’ya da biyan kudin karatunsu, ko kula da su idan sun yi yawa da tsammani mai karfi a kan hakan, ko kuma tsoron ciyar da su, duk da akwai sabani tsakanin malamai kan na karshe.

Hukuncin Kayyade Iyali A Shari’a

Amma hukuncin Kayyade iyali, kamar yadda aka yi nuni kala biyu ne; wanda ya shafi daidaiku da kuma wanda ya shafi mutane gaba daya. Wanda ya shafi dan Adam gaba daya shi ma kala biyu ne:-

 Na daya; Tsara Iyali wato daina haihuwa zuwa wani dan lokaci. Na biyu; Tsayar da haihuwa lokaci mai dan tsawo ta yadda za a tsayar da haihuwa a daina samar da dan Adam a Duniya wani lokaci. Amma idan ya kasance da ma’anar tsayar da samar da dan Adam ta yadda halittar dan Adam zata kare ne wannan tabbas haramun ne a shari’a, amma da ma’anar da aka ambata ko kuma daidaikun mutane su tsayar da haihuwa da kansu ta yadda zasu daina haihuwa wannan babu dalili a kan haramcinsa, a bisa ka’ida wannan halal ne.

Wasu jama’a sun haramta hakan saboda wasu dalilai kamar haka: Idan hakan ya zama hakki ne a hukuncin daidaikun mutane to don me ba zai zama hakki ne na al’umma ba? ga shi kuwa hakkin al’umma ya fi hakkin iyaye karfi musamman a wannan zamani na gasar fifiko da karfi tsakanin al’ummu.

Amsa a kan haka ita ce: Kasancewar wannan hakkin cewa hakkin ne na tilas a kan iyaye babu dalili na shari’a a kansa, saboda haka ba abin da zai hana su kayyade ‘ya’yansu duk sa’adda suka ga dama. Tare da sanin cewa inda zai kai ga rasa dan Adam ne a duniya yake kai wa ga haramun, amma in ba haka ba babu wani dalili a kan haramcin. Kuma yana iya zama abin so idan yawan mutane ya kai ga wani mummunan matsayi a duniya kamar lalacewar tsarin kasashe, da fitina mai yawa, da yawan ne ya haifar da ita.

Dalili na biyu da suka kawo shi ne; Littafi da Sunna sun kwadaitar a kan yawaita haihuwar dan Adam. Amsa ita ce: Wannan kwadaitawar ba ta kai haddin wajabci ba da lizimci saboda haka mutane suna da ikon kayyade ko tsara iyalinsu kamar yadda suka ga dama. Balle ma idan ya kai ga lalacewar tsarin zamantakewar al’umma a nan maganar kwadaitarwa tana karfafa zuwa ga wajabtawa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next