TSari Da Kayyade Iyali



Tsari Da Kayyade Iyali (A Musulunci Da Dokoki)

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Shi ne yake da mabudan sammai da kasa, yana shimfida arziki ga wanda ya so, kuma yana kuntatawa. Lalle ne shi masani ne ga dukkan komai.[1].

Gabatarwar Mawallafi

A wannan karon mun yi duba ne zuwa ga batun ra'ayoyi game da al'amarin Kayyade Iyali da Tsara Iyali kamar yadda Ustaz Muniru Muhammad Kano a watan Rajab mai albarka da ya gabata ya nemi hakan daga garemu. Saboda ya zama mai amfani ga mutane gaba daya, da kuma kara bincike a matakin wannan zamani game da mahangar kasashe da ma wasu addinai da dokokin mafi yawancin kasashen Duniya a yau kan al'amarin Kayyade iyali ko tsara su, da bayanin hanyoyin da a kan bi wajan gudanar da Kayyade Iyali, da batun halarcinsu a musulunci a mahangar malamai.

Duk da cewa ina da karancin lokaci da ya yi mini yawa amma na ga cewa yana da kyau in dan gutsuri wani lokaci domin gabatar da wannan aiki mai nauyi kuma mai amfani a daya bangaren, muna fatan Allah ya sanya shi mai amfani ga al'umma gaba daya.

Kammala littafin ya zo daidai ranan wafatin Uwar muminai Sayyida Khadijatul-Kubra (A.S) wato a ranar laraba 10 ga Ramadan 1424HK, Daidai 5 Nuwamba 2003M, kuma 14 Aban 1382 HSh, muna fatan Allah ya karba daga garemu kuma ya sanya ladan kyauta gareta.

                         Hafiz Muhammad Kano Nigeria

hfazah@yahoo.com



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next