TSari Da Kayyade Iyali



Muna iya cewa; Kiristanci Addini ne da yake da karancin hukunce-hukunce kuma yake himmantuwa da tsarkake kai, ba ya himmantuwa da al’amuran duniya, kamar yadda yake ciko ga addinan ‘ya’yan Isra’ila, shi ya sa suka bar mafi yawan shari’a ko ma dukkanta suka fuskanci bangaren zuhudu da soyayya da rangwame.

Mahangar Salih Al-Wirdani

 Amma Salih Al-wirdani a littafinsa na Asshi’a Fi Misra a shafi na 197 yana fada cewa[16]:

Ba ya halatta zubar da ciki a kowane lokaci matukar ya shiga, mace tana iya amfani da duk abin da zai iya hana ta daukar ciki, idan ba zata iya tarbiyyar ‘ya’yanta ba, ba abin da zai hana ta kayyade iyali da yanke haihuwa.

Mahangar Bakir Sharif Al-Kurshi

Amma Bakir Sharif Al-kurshi a littafinsa na Tsarin Siyasa a musulunci a shafi na 246 yana kawo tsarin tafiyar da al’amura a musulunci ne, zamu yi kokarin kawo wasu daga cikinsu a nan saboda ya shafi abin da muke magana a kai ta wani bangare[17]. Ya ce: Abubuwan da daular musulunci ta ginu a kansu na siyasarta ta cikin gida su ne:

1.      Tsayar da adalci

2.      Kawar da talauci

A cikin wannan a bayanansa ya kawo cewa malaman tattalin arziki sun tafi a kan wajabcin kayyade iyali domin tsoron yawaitar mazauna duniya da kuma tsoron kada dan Adam ya kasa zama nan gaba a duniya. Ya ce: Amma tsarin musulunci ya yi kokarin maganin wannan matsala ta hanya mai sauki wacce ba ta jawo wani halaka ko cutarwa ga kowane mutum daga al’umma sabanin yadda tsarin duniya yake a yau. Hakika tsarin tattalin arziki a musulunci ya wajabta yada yalwa tsakanin al’umma da lamunce rayuwarta, bai bayar da wata mafaka ba ga talauci da rashi da rashin kwanciyar hankali.

Ya ce: Ikbal yana cewa: Bincikena bayan na karanta shari’ar musulunci karatu mai zurfi mai tsawo ya kai ga cewa; duk inda aka fahimci wannan shari’a fahimta mai kyau kuma aka aikata ta kamar yadda ya kamata to hakkin rayuwa zai zama mai sauki ga kowa.

Ya ce: Matsalar burodin ci tana dada ci gaba, sai dai da dacewar Allah mun sami warwara a cikin shari’ar musulunci da hukunce-hukuncenta. Ya ci gaba da cewa: Zai nuni da wasu daga cikin hanyoyin dalla-dalla:

1.      Aiki tukuru domin samar da kayan masarufi, daga abubuwan da kan sanya tabbatar hakan su ne: -



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next