TSari Da Kayyade Iyali



Da farkon farawa muna iya cewa talauci ya mamaye duniya, amma yawan haihuwa sai karuwa yake yi, kusan haihuwa a yau ta ninka mutuwa sau 1,000,000 (miliyan daya) a cikin kowane kwana biyar, kuma ga mafi yawan mutanen duniya duk sai tarewa suke yi a Manyan Birane suna barin kauyuka, abin da kan jawo gwamitsin mutane a Manyan birane da cunkoso.

A bisa binciken Masana idan an tattara dabbobi a waje daya suka samu cunkuso maras ma’ana to shekarun balaga suna karawa sama, wato ba sa balaga da wuri, kuma tazarar da ke tsakanin samun ciki tana daduwa, wato ba sa samun ciki da wuri, kuma mutuwar ‘yan kanana tana daduwa, abin da kan sanya daduwa da karuwa ta ragu ta rika tafiya a hankali. Amma ga mutane abin sabanin haka ne, ba kamar yadda na dabbobi yake ba ne.

Kafin lokacin Juyin masana’antu, a Kasar Ingila da zaran an yi aure to ana sauraron a ga an samu da ne tsakanin ma’aurata, amma yawanci amarya tana haihuwa ne a shekararta ta ishirin ko ishirin da ‘yan kai. Amma a Duniya ta uku yawancin gidaje na dangi ne ba kawai miji da mata ba, a kan yi wa ‘yan mata aure a shekarun farko kamar shekara goma da ‘yan kai. Misali; Mutanen daji ko makiyaya na daji na kabilar Kung a al’ummar San da ke Afrika ta kudu ba sa amfani da Kayyade Iyali, amma suna ba da tazara kamar ta watanni 44 da kuma kawo ‘ya’ya kamar hudu ko biyar Duniya.

An yi hasashen cewa a sama da shekara dubu goma da suka wuce mutanen Duniya ba su kai miliyan goma ba 10,000,000. kamar yadda a farkon shekarun miladiyya ba su wuce miliyan dari uku ba 300,000,000. Amma sai ga shi a tsaka tsakin shekarar 1980s sun wuce miliyan dubu biyar 5,000,000,000 abin da ya sanya jawo hankalin duniya ga tunanin daukar kwakkwaran mataki da kuma shirya Tsarin Iyali.

Tarihin Tsarin Iyali

Rubutattun Takardu sun nuna cewa tun da can akwai Tsarin iyali da Kayyade iyali a tarihin dan Adam, da kuma irin magunguna na itace da sukan yi amfani da shi, ko kuma wasu hanyoyi daban-daban, idan ka duba tarihin kasar Masar da likitocinta a shekarar 1550 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) zaka ga cikakken sako game da hakan. Kamar yadda hadisan Annabi (S.A.W) sun nuna cewa larabawa ma tun da can suna Azalu kafin zuwan Musulunci da shekarun da ba a san farawarsu ba takamaimai. Da yawa marubuta daga likitocin larabawa a karni na goma sun ambaci Tsarin Iyali kamar Alrazi da Ali dan Abbas da Ibni Sina.

 A rubuce-rubucensu sun kawo wasu hanyoyi uku da sukan hana daukar ciki kamar share ruwa daga farji bayan saduwa wanda wannan hanya koda ta dace a hankalce amma ba ta magani. Hanya ta biyu da takan yi maganin hana daukar ciki, akwai tsammanin a samu dacewa, hanyar ita ce hanyar shan magunguna ayyanannu kamar zuma da alimun da sauran hadin lactic acid a matsayin abubuwan da zasu kare kulluwar mani. Ta uku kuwa ita ce hanyar gargajiya, shi ne bayan saduwa ba jinkiri mace ta yi tsalle sau bakwai tana yin baya da baya, ita ma ba kasafai takan yi magani ba.

A kusan shekarar 1900 kusan duk wata hanya ta hana daukar ciki da take a Duniya ana amfani da ita a wannan lokaci, farkon abin da aka karfafa a wannan zamani shi ne amfani da Kondom wanda ana yin sa daga hanjin dabbobi ne domin hana mani isa mahaifa wanda Baitaliye Gabriel Fallopius ya siffanta ya gano a shekarar 1564. Amma Charles Goodyear a shekarar 1839 ya gano narka roba da yadda ake yin Kondom da ita, al’amarin da ya jawo juyi babba da saukakawa wajan amfani da Kondom domin gudanar da tsarin Kayyade iyali. Kuma Kondom ya zama babbar hanyar da ake amfani da ita domin gudanar da tsarin Kayyade iyali tun kusan rabin karshe na karni na goma sha tara.

A kwai bayanai da dama na hanyoyi daban-daban da wadanda suka kirkiro su da ba zamu samu damar kawo dukkansu ba da suka hada da hanyar da Bajamuse F.A. Wilde ya kirkiro a 1823, da kuma bayanai game da amfani ko rashin amfaninsu. Kamar yadda wani Ba'amurke mai binciken magunguna ya gano hanyar kulle wa mace fallopian tubes a garin Ohio a 1881. Amma sauran bayanai wadanda suka shafi tarihinsa a musulunci zamu kawo su ne a bayanan hukuncinsa a musulunci.

Hanyar Zubar Da Ciki



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next