TSari Da Kayyade Iyali



5- Amfani da kwayoyin hana daukar ciki ko allura: Wannan hanya ce da ta yadu a duk duniya.

6- Hanyar lissafin kwanakin haila: Ita ce, Lissafin kwanakin haila da masani Ojino ya gano ta hanyar lissafin kwanakin hailar mace da tabbatar da tsayayyun kwanakinta domin gano kwanakin da kwanta yake sauka, sai a nisanci wadannan kwanakin da kwana biyu kafin da bayan saukar kwan. Wato idan mace tana da haila tabbatarciya mai ayyanannun kwanaki tsayayyu to wannan matar ita wannan hanyar take yi wa amfani banda sauran mata. Sai a san kwanakin da take haila, to daga ranar da take fara haila zuwa ranar sha biyu ba ta daukar ciki amma daga sha biyu daga ranar da ta fara haila zuwa sha shida to a wannan kwanaki tana iya daukar ciki sai a nisanci kusantarta.

1 (11,12,13,14,15,16, 17) 30

Kwanakin daukar ciki

Kwanakin wata kwana talatin daga ranar da mace ta fara haila idan mai haila tabbatacciya ce ta fuskacin lokaci da adadin kwanaki.

7- Hanyar Amerikawa: Ita ce hanyar amfani da wasu kwayoyi kewayayyu da a kan sanya su cikin mahaifa suna da yanayi daban-daban kewayayyu ko kamar kulli-kulli da a kan sa a mahaifa don hana daukar ciki. Wannan hanya ana amfani da ita tun lokacin Arasdo ga dabbobi, amma da aka jarraba a kan mutum bai yi aiki ba, Jamusawa sun aikata ta su ka bari da suka ga cutarta tafi amfaninta. Kamar yadda wani Bajafane ya gano ta ta yadda take amfani sai suka ci gaba da amfani da ita, amma daga baya Amerikawa su ne suka ci nasara sosai a wannan hanya, idan an cire wannan kwayoyin halittar to bayan wata biyu ana iya daukar ciki.

Wannan su ne hanyoyin da ake amfani da su wajan kayyade ko tsara iyali kuma ta yiwu akwai wasu hanyoyin da mu ba mu sansu ba da duniya mai nisa ko maras cigaba take amfani da su.

Matsayin Hanyoyin

Yawancin wadannan hanyoyi da ake amfani da su musulunci ya halatta su sai dai wasu daga ciki da shari’a ta haramta kamar zubar da ciki da kuma ganin farjin muharramar mace ko ajnabiyya. Kuma dukkan abin da ba a haramta ba halal ne sai dai idan zai kai ga aikata haram.

Wato wadannan ka’idoji ne da ake amfani da su a Ilimin Usul da cewa komai halal ne sai dai abin da aka yi bayani kan haramcinsa[4]. Wannan ka’ida ce da aka tabbatar da ita a Kur’ani da hadisan Manzo (S.A.W) Saboda haka duk sa’adda babu wani dalili kan haramcin kayyade iyali ko tsara su ta daya daga wadannan hanyoyi to ya halatta a aiwatar da ita.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next