Imamanci Da Nassi



Sannan sai ya amsa da cewa: Da wasiyya ta kasance wajibi da Manzo (S.A.W) ya yi, alhalin bai yi wasiyya ba, Umar ma bai yi ba[20].

Yayin da Ibn Hazam ya ci gaba da kawo nazarinsa sai ga shi yana kore asalin nazarin shura da kuma kore maganar hakkin zabar shugaba ta hannun manyan al’umma, yana mai dogaro da zabar halifa ta hanyar nassi! Saboda ya nutsu da wajabcin nassi, sai dai shi yana nufin nassin da ya yi daidai da abin da ya faru, koda yake babu wani dalili a kan hakan.

Hakika nassi bai saba da asalin nazarin shura ba har abada, shura a nan ba al’amari ne da ba shi da abin da ya kebance shi da wani yanayi ba, kuma dattijan al’umma ba su da hakkin su zabi wanda suka so haka nan kawai ba wani dalili, domin shura tana da iyaka, wannan kuma iyakar nassi ne ya zana mata ita.

Suka ce: Daga sharadin shugaba ya kasance bakuraishe, imamanci ba zai yiwu ba sai da shi, suna masu kafa dalili da nassi tabbatacce a kan haka, hakika ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Imamai daga Kuraish ne”. A wata ruwaya yana cewa: “Ku gabatar da Kuraish kada ku shiga gabanta” tare da samun wadannan nassosi da kowa ya sallama a kansu babu wata shubuha ta mai jayayya[21], ko zancen mai sabawa da za a yi la’akari da shi.

Suka kuma shardanta wa wannan bakuraishe ya zama na ainihi daga kabilar Bani nadar dan Kinanata, domin ya yi daidai da nassi[22].

Ahmad dan Hanbal ya ce: “Ba yadda za a yi wani daga wanin kuraishawa ya zama halifa[23]”. Yana mai kafa dalili da wannan hadisi da tawaturinsa, da kuma fasawar da Ansar suka yi suna masu mika wuya ga muhajirai kuraishawa yayin da suka kafa musu dalili da wannan hadisi a Sakifa[24].

Ibn Khaldon ya ce: Jamhur sun tafi a kan sharadin kuraishanci da kuma ingantuwar halifanci ga bakuraishe koda kuwa ba zai iya daukar nauyin aikin tafiyar da al’amuran musulmi ba[25]. Haka nan nassin shari’a ya tabbatar da tawaturin magana a kan ingancinsa kuma ijma’i a kansa ya tabbata.

Abu ne bayyananne cewa wannan ya faru ne yayin da nasara ta tabbata ga nassi a kan asasin shura, yayin da halifa na biyu ya ga wajabcin samuwar nassi a kan wanda zai maye gurbinsa. Sai wannan nassi ya zama ya hade da tsarin siyasa, duk da yana jefar da ka’idar shura gaba daya.

Hada da cewa nassin hadisin Annabi mai daraja da daukaka yana cewa: “Shugabanni daga kuraishawa ne” yana mai rushe tunanin shura gaba daya! Sai ya zama wanda ya yi galaba a kan al’umma ya kuma kwace halifanci da takobinsa ya zama bakuraishe halifancinsa ya inganta domin bai fita daga nassin da ya gabata ba.

Haka nan ba a la’akari da sharuddan wajibi da suke dole a same su ga halifa kamar ijtihadi, da adalci, da takawa, domin idan halifa ya zama bakuraishe to halifancin sa ya inganta koda kuwa ya zama mai rauni ko azzalumi. Ashe kenan al’amarin shura ya kamata ya zama ya fita daga wajen nassi, kuma ba zai yiwu a zabi wani ba sai bakuraishe na asali.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next