Imamanci Da Nassi



A takaice wannan mas’ala tana tabbatar mana da samuwar nassi ingantacce a wannan nazari ta wannan hadisi: “Shugabanni daga kuraishi ne” hakika Buhari da Muslim da ma’abota Sunnan da Siyar sun rawaito da lafazi mabanbanta, sai dai wannan nassi yana bukatar abin da zai kebance shi saboda wasu dalilai:

1-Nassin da ya gabata “Shugabanni daga kuraish ne”, shi kadai ba ya iya tabbatar da hadafin da ake nema na tabbatar da shugabanci, wannan ya kasance domin kare addini da al’umma, ta yadda sahabbai da kansu sun fahimci wannan al’amari tun karewar zamanin halifanci na gari.

A cikin sahihul Buhari ya zo cewa: Yayin da aka yi jayayya tsakanin Marwan dan Hakam yana Sham, da Abdullahi dan Zubair yana Makka, sai wasu jama’a suka tafi wajen sahabi Abi barzatal aslami suka ce: Ya Aba barza! ba ka ganin abin da mutane suka fada cikinsa? Sai ya ce: Ina neman ladan Allah domin na wayi gari ina mai fushi da kuraishawa, domin wanda yake a Sham wallahi ba yana yaki ba ne sai domin duniya, wanda yake yaki a Makka ba yana yaki ba ne sai domin duniya[26].

2-Akwai wasu nassosi ingantattu da suka kebance hadisin da ya gabata, kamar haka: Hakika Annabi ya tsoratar a kan alfahari da nasaba ta kuraish, ya kuma yi gargadin cewa wannan al’umma zata halaka, kuma al’amarinta zai daidaice. Ya zo a cikin Sahilul Buhari, daga gare shi (S.A.W) ya ce: “Halakar wannan al’umma zata kasance a hannun wasu samari na kuraishawa ne”[27].

Yaya kenan za a iya hada wannan nassosi guda biyu mai cewa: “Shugabanni daga kuraish ne” da kuma “Halakar wannan al’umman zata kasance a hannun wasu samari na kuraishawa ne”. Ba makawa a kebance wannan hadisin da abin da ya zo na hadisai game da kuraishawa, wannan kuma kebancewar iri biyu ce:

A-Ta korewa: Akwai hadisai da suka toge wasu mutane daga kuraishawa kuma suka nisantar da su daga fagen girmamawa.

Ibn Hajar Alhaisami a wani hadisi mai sanadi ingantacce cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Mafi sharrin kabilun larabawa: Banu Umayya, da Banu Hanifa, da Sakif”.

Ya ce: A wani hadisi ingantace Hakim ya ce: A bisa sharadin shaihaini daga Abi Barzata ya ce: “Mafi kin jama’a ko mutane a wajan manzon Allah su ne Banu Umayya[28]”. Abin da ya zo game da sukan alayen Hakam baban Marwan yana da yawa kuma mash’huri ne, shin ya inganta shugabancin al’umma ya dogara da mafi sharrin kabilun larabawa wanda sune ma fi kin mutane a wajan manzon Allah (S.A.W)!

Idan wadannan suka zama masu hukunci a sarari to dole mu shaida da cewa lallai al’umma ta halaka ta karkace ga barin gaskiya, kuma kamata ya yi al’umma ta dawo zuwa ga bin shiriyar manzon Allah (S.A.W) da nassin da ya kawo daga Allah na wasiyyarsa da Ahlin gidansa (A.S) maimakon ta koma tana neman samar wa abin da ya faru mafita da kuma tawilinsa da nassi.

B-Ta tabbatarwa: Hadisin da yazo yana mai nuna fifikon kuraishawa da zabi a kan sauran kabilu bai tsaya ga nuna da’irai kuraishawa ba kawai, sai dai ya kebance wannan da cewa wasu jama’a daga cikinsu ake nufi sai ya ce: “Allah ya zabi Kinana daga ‘ya’yan Isma’il, ya zabi Kuraish daga Kinana, ya zabi Bani Hashim daga Kuraish, ya zabe ni daga Bani Hashim”[29]. Wannan fifita wa da daukaka ga Bani Hashim a kan sauran kuraish ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next