Imamanci Da Nassi



Ibn Taimiyya yana mai karin bayani game da wannan hadisi yana mai cewa: “Ya zo a cikin Sunna cewa; Abbas ya kai karar wasu kuraishawa da suke wulakanta shi, sai Manzo (S.A.W) ya ce: Na rantse da wanda raina take ga hannunsa! Ba wanda zai shiga aljanna sai ya so ku don Allah da kuma kusancina”. Idan sun kasance su ne mafifitan halitta to ba makawa ayyukansu su ne mafifita ayyuka, mafificinsu shi ne mafificin kowane mafifici na sauran kabilun kuraishawa da larabawa, har da Bani Isra’il da waninsu[30].

Matsayi a nan ba matsayi ne na fifita wa ba shi ke nan, sai dai abin nufi kuraish imaninta ba ya inganta sai ta so su Bani Hashim so biyu; Saboda Allah da kuma domin kusanci da Manzo (S.A.W).

Shin ya inganta kuraish gaba dayanta ta zama daidai a wajan gabtarwa a shugabanci da imamanci, kuma akwai Banu Hashim da nassi ya daukaka su zuwa mafi daukakar matsayi, da akwai kuma Banu Umayya da nassi ya kaskantar da su zuwa mafi kaskancin martaba?!

Idan abin da ya wakana ya kai mu zuwa ga wannan halin, to shi kenan sai mu shaida da cewa abin da ya faru kauce wa daga hanya ta gari ne, ba mu yi kokarin gyara shi ba.

A takaice yana iya bayyana a fili cewa, a nan mu mun yi duba sosai don gane da abin da ya shafi bahasin maudu’in imamanci, sai muka ga cewa dalilin da ya sa aka samu wannan cece-kuce dangane da wadannan sabani da ake ta fama da su shi ne, bin wannan al’amari da ya faru, da kuma kokarin gyara shi da kuma sanya shi doka da madogara na asasi a tsarin siyasa da tafiyar da shugabancin al’umma har ya zama doka.

Maganganu masu rusa juna da ake samu a lokuta daban-daban sun bayyana a zahiri a wadannan ra’ayoyi, abin da ya sa suka rasa kimarsu a matsayinsu na nazarin musulunci da zai iya warware daya daga manyan al’amuran musulunci masu girma.

Sai ga magana game da nassi na shari’a ba ta tsaya ga shi nassin ba, ba ta kuma lizimtu da aiwatar da sharuddansa ba da iyakokinsa. Shura kuma an nuna cewa abu ne rusasshe da aikin da halifa da ya gabata ya yi na nassi ga mai bi masa, da kuma ra’ayin shura da ra’ayin kwace da rinjaye da karfi da kuma sa karfin takobi. Amma mahangar tsarin shawarar manyan gari (shura) shi ya fi kowanne daga wadannan mahangai shiga duhu.

Wani lokaci sai ta zama hannun mutum daya da zai kafa kansa halifa mutum biyu su bi shi kamar yadda ake daura aure, ko mutum hudu su bi shi, ko kuma su zama shida da halifa da ya rigaya zai ayyana ba tare da al’umma tana so ba, kai har abin ya wuce hakan, kai har malami kamar Ibn Khaldon ya sanya makusantan sarki da na gefensa -komai kuwa rashin takawarsu da iliminsu - a matsayin ma’abota kulla shugabanci da warwarewa wadanda irinsu ne suka sabawa halifa Ma’amun kan sanya halifanci zuwa ga Ali Arrida (A.S)  bayansa[31].

Wannan al’amari ya faru a rabi na biyu na halifancin Usman, ta yadda ya zamana an samu shugaban masu bayar da shawara wani ne daga makusantansa na Banu Umayya a kebance, wanda ba su da wani fifiko, da daukaka, da kokari, da rigo na addini, tare da yawan wadanda suke da wadannan dabi’u a wannan lokaci!

Sai manyan shura suka zama su ne Abdullahi dan Amir, da Abdullah dan Sa’ad dan Abi Sarh[32], da Sa’id dan Asi, da Mu’awiya dan Abi Sufyan, da Marwan dan Hakam.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next