Imamanci Da Nassi



Mai girma da daukaka yana cewa: “Yana tsarkake su yana sanar da su littafi da hikima”[9].

Idan hadafin halittar mutum ya zama shi ne bauta ga Allah, ga shi kuwa a bisa dabi’arsa an sanya masa damfaruwa da wasilar da zata kai shi zuwa ga kamala, domin shi yana karkata zuwa ga kamala da sonsa na fidira, da muhimmancin annabta domin bayanin hanyoyin wannan shiriya, kuma da bayyana hakikanin gaskiya da takan kai zuwa ga wannan kamalar.

Idan haka ne al’amarin yake to menene zai sa bukatar cigaban wannan hadafin da mikuwar wannan sako ya zamanto ta hanyar imamanci da Shi’a suke shardanta nassi a cikinta, da sauran sharudda kamar ilimi na baiwa daga Allah, da kuma isma?

Amsa a kan wannan tambaya da waninta na daga tambayoyi yana tilasta mana tambayar kawukanmu kamar haka;

Menenne imamanci a mahangar addinin Allah?

Menene muhimmancinsa?

Bayan mun fita daga mahallin jayayya zai iya yiwuwa mu amsa wannan tambayoyi da suke zowa kwakwalwa game da imamanci da sharuddansa da suka hada da ilmi, da isma, da makamancinsu na daga sharudda na dole a same su ga imami.

Mahallin Sabani Tsakanin Mahanga Biyu

Imamanci da halifanci a makarantun Sunna suna da matsayi daya da suka fuskanta da yake bayar da karfi a kan cewa, imami kuma halifa bayan Manzo (S.A.W) yana nufin shugaba, kuma jagora na siyasa da yake tafiyar da sha’anin tsarin musulunci bayan wafatin Manzo (S.A.W).

A kan wannan asasin babu wani dalili na sanya jagora ya zama yana dogara da nassi da ayyanawa ta fusakacin Allah da kuma bayanin Manzo, al’amarin an bar shi ne ga al’umma ta zabi wanda ta so ta ga ya cancanta ga tsayuwa da wannan al’amari na jagoranci, domin muhimmancin imami kuma halifa a nazarin wannan koyarwa, ba ya wuce aikin jagorancin siyasa da tafiyar da al’umma ta fuskacin haddodi, kuma yana daga abu na hankali a wannan hanya al’umma ta tsayar da halifa ya zama ta hanyar shawara (shura), ko kuma ta hanyar wakilan  al’umma, ko ta hanyar gado.

Ya rage mu san menene sharuddan da suka wajaba ga halifa da aka zaba, haka nan zamu iya gani a wannan mahanga ta Ahlussunna suna ganin imamanci da halfanci bayan Manzo jagoranci ne na siyasa shi kenan, saboda haka ya isa ya zama wannan mutumin adali ne ta nahiyar aiki kamar yadda aka sani, kuma ba a shardanta masa ya zama yana da isma da ilimi da Allah ya ba shi ba, ya isa ya zama yana da iko da zai kai shi wannan matsayi a tsarin musulunci.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next